ANNABI DA SAHABBANSA // 007



_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_

         ANNABI DA SAHABBANSA // 007
.
_Dabi'unsu: Duk Da Wasu Ayyuka Munana Da Muka Ambato Na Larabawa A Zamanin Jahiliyya Bai Hana Kuma A Kalli Kyawawan Dabi'unsu Ba Wadan Da In Ka Kalla, Kuma Aka Ce Maka Nasu Ne Za Ka Yi Matuqar Mamaki, Misali:-_

_*1) Karamci:* Abu Ne Mai Sauqi Ka Sami Balarabe Talaka Fayau Bai Da Komai Sai Raqumarsa Da Yake Tatsa, Amma In Ya Yi Baqo Bai Da Abin Da Zai Ba Shi, Sai Ya Soke Raqumar Don Dai Ya Kyautata Masa._
.
_Sau Tari In Kana Karanta Waqoqinsu Za Ka Taras Suna Alfahari Da Karamci, Suna Yabon Kawunansu Da Shi, Har Su Fifita Kawunansu A Kan Sauran Dauloli Kamar Iran Da Rum, Ko Giya Da Suke Alfahari Da Ita Ba Don Sun Dauke Ta Wani Abu Ba, Don Tana Sauqaqa Yin Kyauta Ne, Ko Caca Ma In An Ci Nasara Talakawa Ake Ba Su Kudin, Shi Ya Sa Qur'ani Ya Ce Suna Da Amfani Amma Zunubinsu Shi Ne Gaba._
.
_*2) Cika Alqawari:* Cika Alkawari A Wurinsu Tamkar Addini Ne, Sun Riqe Shi Tamau, Mutum Bai Damu Da Ya Rasa 'ya'yansa Ba, Ko Ya Rusa Gidansa A Kan Alqawari, Ga Qissoshi Nan Nasu Daban-daban Wadan Da Muka Karanta A Kan Dabi'unsu._

_*3) Jajurcewa: In Suka Yi Niyyar Yin Wani Abu Sukan Jajurce Komai Qamari Kuwa, Ba Abin Da Zai Dakatar Da Su Ko Ya Hana Su._
.
4) Izza: Kowa Na Ganin Ya Fi Qarfin Wulaqanci, Kuma A Shirye Yake Ya Fuskanci Duk Wani Abin Da Zai Dumfaro Shi, Wannan Ya Janyo Musu Wuce Gona Da Iri Wajen Nuna Jarumta, Mummunan Kishi, Saurin Daukar Mataki, Duk Lokacin Da Suke Ganin An Raina Hankalinsu Nan Take Za Ka Ga Sun Jawo Takubba, Kuma Ba Su Damu Da Mutuwa Ba In Don Wannan Abin Ne.
.
5) Ko Banza Dai Dole A Sifanta Su Da Kadaituwa Da Qauye Gami Da Rashin Sirkuwa Da Al'adun Da Ba Nasu Ba, In Ba Wadan Da Suka Yi Maqwabtaka Da Wadancan Manya-manyan Dauloli Da Muka Lissafo A Baya Ba, Wannan Ya Sa Suka Iya Tsare Gaskiyarsu, Da Amanarsu Gami Da Kauce Wa Yaudara Da Ha'inci, Duk Da Munanan Dabi'un Da Muka Fadi In Muka Dubi Wadannan Za Mu Ga Cewa Zai Yi Wahala A Sami Kamarsu A Duniya.
.
Al'ummar A Watse Take, Kowa Sha'anin Gabansa Yake Yi, Babu Doka Ba Oda, Amma Har Da Haka Iyakacin Abin Da Suka Aikata Kenan, Yanzu Dubi Sauran Larabawan Da Suka Tasirantu Da Wasu Daulolin Ka Ga Yadda Suka Mai Da Jinin Dan Adam, Misalin Yaman, Syria Da Iraqi, Za Su Iya Yin Komai A Kan Mulki, Tarihi Ya Nuna Mana Cewa Ko A Zamani Jahiliyya Abu Sufyan Ya Qi Yarda Ya Yi Qarya Duk Da Tsananin Buqatarsa A Wajen Sarkin Habasha, Allah Shi Ne Mai Hikima Da Ya Sanya Annabin Qarshe A Cikin Wannan Al'ummar.
.
Muhammad Saw: Wannan Shi Ne Annabi Na Qarshe A Cikin Jerin Annabawan Da Allah Sw Ya Turo A Qarshen Zamani, Malaman Tarihi Sukan Inganta Nasabarsa Zuwa Adnan Ne Kawai, Wasu Kuma Suna Ganin Ingantaccen Tarihinsa Ya Kai Har Zuwa Ibrahim As, Wanda Dai Ake Ganin Akwai 'yan Matsaloli Shi Ne Daga Ibrahim As Har Zuwa Adam As, Sai Dai In Muka Ce Za Mu Lissafo Duka Danganen To Gaskiya Zai Gajiyar Da Mai Karatu, Amma Akwai Su A Littafan Tarihi.
.
_Dangin Annabi Saw Sun Yi Fice Da Sunan Banu-hashim, Kuma Shi Hashim Din Kamar Yadda Muka Fadi A Baya Shi Ne Ya Ci Quri'ar Zama Mai Riqe Da Makullan Qa'aba Gami Da Kula Da Mahajjata, Sunansa Na Asali Amr, Amma Hashim Ya Samu Ne Don Shi Ya Fara Ba Wa Mahajjata Alkubus, In Aka Ce (Hashama) Wato Ya Karkarya Buredi Don Alkubus, Kuma Shi Ne Ya Fara Sanya Su Zuwa Kasuwanci Qasar Sham Kamar Yadda Muka Gani A Suratul Quraish Suna Zuwa Lokacin Zafi Da Na Sanyi.
.
Wata Rana Hashim Ya Nufi Sham Kasuwanci Kamar Yadda Ya Saba, Da Ya Zo Madina Ya Auri Wata Mata Sunanta Salma, Ya Dan Zauna A Wurinta Na Dan Lokaci, A Qarshe Ya Bar Ta A Wurin Iyayenta Ya Wuce Palestine, Bai Dawo Ba Allah Ya Yi Masa Rasuwa A Can, Ashe Ita Matar Ta Sami Ciki, Da Ta Haihu Sai Ta Sanya Wa Yaron Suna Shaiba, Ta Sa Masa Wannan Sunan Ne Don An Haifo Shi Da Furfura A Kansa, Haka Ta Raine Shi A Madina Ba Tare Da Wani Dan Uwansa A Makka Ya San Da Shi Ba.

✍🏽Baban Manar Alqasim
Post a Comment (0)