ANNABI DA SAHABBANSA // 009 .



_*⚖️ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖️*_

      ANNABI DA SAHABBANSA // 009
.
_Wannan Yunquri Na Rushe Dakin Allah Ya Faru Ne A Watan Muharram Da Kwana 55 Kafin Haihuwar Annabi Saw, Wanda Zai Zo Daidai Da Qarshen February Ko Farkon March, Shekara Ta 571 Miladiya, Wannan Zai Iya Zama Shirye-shiryen Turo Wani Manzo A Wannan Yankin, Domin In Muka Dubi Baitul-maqdis Za Mu Ga Cewa Mushrikai Sun Taba Mamaye Alqiblar, Alhali Musulmai Ne Ke Zaune A Wurin, Domin A Sa'innan Kiristoci Su Ne Ke Riqe Da Ragamar Muslunci Kafin A Turo Wani Manzo Wanda Suka Kafirce Masa, Bukhtanasar Ya Mamaye Wurin Da Shekara 587 Kafin Miladiya, Rum Kuma A Shekara Ta 70 Miladiya, Qa'aba Kuwa Allah Ya Tsare Abinsa Ya Halaka Abrahata._
.
_Wannan Lamari Na Halakar Abrahata Ya Faru Ne A Daidai Lokacin Da Komin Kasawar Abu In Dai Ya Faru A Wannan Yankin To Duk Manyan Daulolin Can Guda Uku Za Su Sani, Don Kuwa Habasha Tana Da Kyakkyawar Alaqa Ta Addini Da Qasar Rum, Ita Kuma Iran Ta Kasa Ta Tsare Tana Ta Sanya Ido A Duk Wani Abu Da Zai Sami Rum Da Qawayenta, Hakan Ya Sa Nan Da Nan Iran Ta Yi Wuf Ta Sauka A Yaman, Don Ta Fadi Gasassa, Da Ma Manya-manyan Qasashen Da Suka Ci Gaba Kenan A Wancan Lokacin Wato Rum Da Iran._
.
_Wata Hikimar Da Za Mu Iya Hararowa In Dai Qoqarin Rusa Dakin Allah Da Runduna Mai Qarfin Gaske Irin Wannan Za A Ruguza Su Ba Tare Da Wani Motsi Na Yaqi Ba, Tabbas Wani Abu Zai Yi Tasiri A Zuciyar Jama'a, Masamman Na Manyan Daulolin Nan Game Da Matsayin Wannan Daki, Sannan Wata Fassara Kuma Za A Iya Cewa Allah Sw Ya Fifita Barin Dakinsa Mai Alfarma Sama Da Addinin Da Abrahata Yake Dauke Da Shi, Bayan Wannan Abin Da Ya Faru Da 'yan Kwanaki Aka Haifi Manzonsa Wanda Zai Zo Da Sabon Saqo, Don Dama Da Cikinsa A Lokacin._
.
_To Yanzu Dai Abdulmuttalib 'ya'yansa 10, Maza Cikinsu Akwai: Harith, Zubair, Abutalib, Abdullahi (Mahaifin Annabi Saw Kenan) Hamza, Abulahab, Gaidaq Wato Hajla, Muqawwim Wato Abdulka'aba, Suffar Sai Kuma Abbas, Mata Kuma Su 7 Ne: Baida Wato Ummul-hakim, Barra, Atika, Safiyya, Arwa Da Kuma Umaima, Shi Kuma Abdullah Wato Mahaifin Annabi Saw Sunan Mahaifiyarsa Fatima Bint Amr, Allah Sw Ya Sanya Wa Abdulmuttalib Qaunarsa, Sabo Da Kamewarsa Da Hankalinsa, Meyuwuwa Ya Fara Tunanin Shi Ne Zai Gaje Shi._
.
_To Kamar Yadda Muka Karanta A Baya Cewa Ya Yi Bakancen Zai Yi Hadaya Da Dansa Guda Matuqar Sun Cika Goma, Don Haka Ya Tara Su, Ya Yi Musu Bayani, Su Kuma Suka Ba Shi Hadinkai, Sai Ya Yi Quri'a A Tsakaninsu, Sai Quri'ar Ta Nuna Abdullah, Ya Dauki Wuqa Ya Kama Hanyar Qa'aba Da Shi, Amma Sai Kawunnansa Na Banu Makhzum Masamman Dan Uwansa Abutalib Suka Ce Ba Za A Yi Haka Ba, Suka Ba Shi Shawarar A Je Wajen Masana A Samo Mafita, Su Kuma Masanan Suka Ce To A Yi Quri'a Tsakanin Abdullah Da Raquma 10, In Ta Nuna Raquma Sai A Yi Hadayar Da Su, In Kuwa Ta Nuna Abdullahi Sai A Qara Wasu Goman A Sake Buga Quri'ar._
.
_Ilai Kuwa, Haka Aka Yi Ta Sanya Raquma Goma-goma Suna Nuna Abdullah Sai Da Aka Sanya Dari Kafin Suka Fanshe Shi, To Dama Fansar Jini A Wurinsu Raquma 10 Ne, Sai Wannan Lokacin Suka Mai Da Shi 100, Muslunci Kuma Da Ya Zo Bai Canja Ba Sai Ya Bar Shi Haka, Bayan Wannan Lokacin Ne Abdulmuttalib Ya Zabo Wa Abdullah Mata, Wato Amina 'yar Wahab, Auren Zumunta Aka Yi Musu Don Ita Ma Kakanta Abdu Manaf Ne, Tana Cikin Babban Dangi, Sabo Da Mahaifinta Wahab Shi Ne Shugaban Banu Zuhra, Haka Dai Ta Tare A Gidansa Na Dan Wani Lokaci, Wanda A Cikinsa Ne Mahaifinsa Abdulmuttalib Ya Tura Shi Qasashen Sham Don Kasuwanci, Sai Allah Sw Ya Masa Qaren Kwana A Madina._
.
_An Rufe Shi A Gidan Nabigatul Ja'di Yana Da Shekara 25 Kacal, Sannan Ma Ba A Haifi Annabi Saw Ba, Kamar Yadda Mafi Yawancin Littafan Tarihi Suka Fadi, Ya Rasu Ya Bar Raquma 5, Da Wasu 'yan Tumaki, Da Wata Baiwa Bahabashiya Mai Suna Baraka, Wace Ake Kiranta Da Ummu-aiman, Ita Ce Ma Ta Raini Annabi Saw, Za Mu Iya Cewa Haihuwar Annabin Ta Kasance Ne A Safiyar Litinin, A Tara Ga Watan Rabi'ul Auwal, A Farkon Shekarar Da Ake Kira Shekarar Giwaye, Wanda Ya Zo Daidai Da 22 Ga Watan April Shekara Ta 571 Miladiya._
.
_Lokacin Haihuwarsa Ne Mahaifiyarsa Ta Aika Wa Kakansa Abdulmuttalib Cewa Ta Sauka, Ya Yi Matuqar Farin Ciki, Ya Shiga Qa'aba Ya Yi Addu'a Ya Gode Wa Ubangijinsa, Ya Sanya Wa Yaron Suna Muhammad, Wannan Shi Ne Karon Farko Da Larabawa Suka Taba Jin Wannan Sunan, Aka Yi Masa Shayi A Ranar Suna Kamar Dai Yadda Ake Yi Wa Kowani Yaro A Wannan Lokacin, Wace Ta Shayar Da Shi Bayan Mahaifiyarsa Ita Ce Suwaiba, Bararriyar Baiwar Abulahab Da Nonon Danta Masruh._
.
_Kafinnan Ma Ta Shayar Hamza Dan Abdulmuttalib Da Abu-salama, Wannan Zai Ba Mu Hasken Kan Yadda Baffan Nasa Ya Yanke Shawarar Kare Shi Daga Baffanninsa Da Suka Sako Shi A Gaba, Ko Kuma Shi Annabin Yadda Ya Yanke Shawarar Auran Ummu Salaman Bayan Mutuwar Mijinta Abu-salama, Da Irin Matsayinta A Gidansa Duk Kuwa Da Kasancewar Wasu Matan Sun Riga Ta Shiga Gidan._
.
_*✍🏼Baban Manar Alqasim*_
Post a Comment (0)