ANNABI DA SAHABBANSA // 010 .



_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_

        ANNABI DA SAHABBANSA // 010
.
_An Kai Annabi Saw Raino Wani Qauye Kamar Yadda Sauran Iyaye Suke Kai Diyoyinsu, Galibi Babban Dalilin Da Ya Sa Suke Yin Haka Don Su Goce Wa Cututtukan Birni Ne, Sannan Jikin Yaro Ya Yi Qarfi, Alamar Jarumta Ta Bayyana Masa Tun Bai San Buhum Ba, Ya Gwanance A Harshensa Yana Qarami, Wadan Da Suke Iya Ba Da Raino Mawadata Ne, Don Ko Ba Komai Masu Rainon Za Su Riqa Samun Nasu A Dalilin Yaron Da Aka Kawo Musu, Baya Ga Biyan Kudin Raino Ga Ababan Sanyaya Zuciya Daga Lokaci Zuwa Lokaci, Sanin Maraicin Annabi Saw Ya Sa Aka Qi Daukarsa, Suna Ganin Me Za Su Samu?_
.
_A Shekarar Da Aka Dan Sami Qarancin Abinci, Wata Mata Da Ta Fito Daga Qabilar Banu Sa'ad, Wanda Shi Ne Ya Sa Ake Ce Mata Sa'adiyya Wato 'yar Wancan Qabila Ta Sa'ad, Sunanta Halima, Ta Fita Cikin Matan Qabilar Don Neman Dan Raino, Ta Ce: Da Komai Ya Qare Mana Sai Na Fita A Kan Wata Jaka Tawa, Ba Mu Da Sauran Wani Abu, Ga Yaron Da Na Dauko Ya Ishe Mu Da Kuka Sabo Da Yunwa, Qirjin Kuma Babu Nonon Da Zai Ishe Shi, A Tunkiyar Da Muka Dauko Kuma Ba Nonon Da Zai Sha, Sai Dai Muna Sa Rai Cewa Za Mu Sami Mafita A Kan Abin Da Ya Fito Da Mu._
.
_Ta Ce: Haka Muka Shugo Makka, Ba Wace Ba A Yi Mata Tayin Annabi Saw Ba Cikimmu, Amma Da Zarar An Ce Maraya Ne Duk Sai Mu Qi Karba, Mukan Ce "To Maraya Me Na Sama Ya Ci Bare Ya Ba Na Qasa?" Ikon Allah Duk Sauran Matan Sun Sami Wanda Za Su Raina Sai Ni Kadai Ce Na Rage, Har Mun Kama Hanya Sai Na Ce Wa Maigidan "Wallahi Ina Jin Nauyin A Ce Duk Sauran Matan Sun Sami Wanda Za Su Raina Sai Ni Kadai, Gaskiya Zan Koma Na Dauko Marayan Nan" Shi Kuma Ya Ce "Ba Komai Sai Ki Ga Allah Ya Yi Miki Budi A Dalilinsa"._
.
_Ta Ce: A Gaskiya Da Na Sami Wani Da Ban Dauke Shi Ba, Amma Ko Da Na Dauko Shi Na Dora Shi A Kan Cinyata Nan Da Nan Qirjina Ya Cika Da Nono Ya Sha Ya Qoshi, (Kenan Hatta Nonon Da Ya Sha Na Masamman Ne Bai Taras Da Wani Ba, Arziqin Da Ya Ci Sai Lokacin Aka Same Shi Bai Gaurayu Da Qazantar Baya Ba) Dan Uwan Rainonsa Ma Ya Sha Har Ya Yi Barci Wanda A Baya Hakan Sam Ba Ta Samuwa._
.
_Maigidana Ya Leqa Turke Ya Tatso Mana Nonon 'yar Akuyar Da Muka Fito Da Ita, Muka Sha Mu Da Yara Muka Qoshi, Muka Kwana Cikin Yalwa, Kashe-gari Ya Ce Min Mun Dauko Dan Baiwa Fa, Na Ce Allah Ya Sa, Haka Dai Muka Yi Shirin Dawowa, Na Dora Dan Raino A Kan Jaka Ni Ma Na Hau, Wallahi Irin Saurin Da Take Yi Ya Ba Kowa Mamaki, Har Sai Da Sauran Matan Suka Riqa Cewa "Haba Sa'adiyya Ki Dan Tsahirta Wa Mutane Mana! Wai Ba Jakar Da Kike Hawan Nan Ba Ce?" Na Ce "Ita Ce Wallahi"._
.
_Tun Da Muka Dawo Gida Tare Da Yaron Nan Komai Namu Ya Canja, Hatta Qeqasasshiyar Qasar Da Muke Fama Da Ita Ta Fara Karbar Shuka, Bisashe Kuwa Ko Ba Tsiro Sai Ka Ga Sun Yi Kiwonsu Sun Qoshi Sabanin Sauran Na Jama'a, Har Sukan Riqa Cewa A Riqa Bin Mu A Baya, Amma Gaskiya Ba Sa Samun Komai (Kenan Baiwa Ce Ta Masamman)._
.
_Ta Ce: Yaro Sai Saurin Girma Yake Yi Da Lafiya, Da Na Ga Ya Kai Shekara Biyu Na Yaye Shi, Na Koma Da Shi Wajen Mahaifiyarsa Duk Da Cewa Muna Tsananin Buqatarsa Sabo Da Abubuwan Alkhairai Da Muke Gani, Da Na Kai Shi Sai Na Ce Wa Gyatumarsa "Da Ba Ki Bar Min Dana Ya Dan Qara Girma Ba? Gaskiya Ina Ji Masa Tsoron Annobar Cikin Garin Makka" To Ba A Jima Ba Ma Ta Dawo Da Shi, Haka Annabi Saw Ya Zauna Da Banu Sa'ad Har Shekara 4-5 Inda Maganar Tsagar Qirji Ta Taso._
.
_Muslim Ya Rawaito Wani Hadisi Ta Hanyar Anas Cewa: (Jibril Ya Zo Wa Annabi Saw Lokacin Yana Wasa Da Yara, Ya Kama Shi Ya Kwantar Da Shi, Ya Fede Shi, Ya Hankatso Zuciyarsa, Ya Ciro Gudan Jinin Da Yake Ciki, Ya Ce Wannan Ne Rabon Shaidan, Ya Wanke Da Ruwan Zamzam A Cikin Tasa, Sannan Ya Mai Da Ita Kamar Yadda Take, Yara Kuma Suka Ruga Suka Gaya Wa Mamansa Cewa An Kashe Shi, Da Ta Zo Sai Ta Ga Wani Haske Yake Yi). Wannan Abu Ya Razanata, Don Haka Ta Dauke Shi Ta Mai Da Shi Wurin Mahaifiyarsa, Haka Annabi Saw Ya Zauna Tare Da Mahaifiyarsa Har Sai Da Ya Kai Shekara Shida._
.
_*✍🏼Baban Manar Alqasim*_
Post a Comment (0)