BIYAN BASHIN KADDARAR KAUYE

BIYAN BASHIN KADDARAR KAUYE



Tuki nake cikin taraddadi a tsohon babur di na kirar vespa zabuwa mai doro. Ni dai fata na na isa inda aka aike ni na dawo lafiya, ala barshi sai na fito fili na fadawa Oga gaskiyar lamari. Idan na yi sa’a ya faranta mini kamar yadda na faranta masa a aiken da ya yi min. Na san halin maigidanmu sarai, idan kana neman wata alfarma sai ka bari bayan ka yi masa wani aikin da ya ji dadi tukunna ka tambaye shi.

Babur din tsoho ne tukuf, idan abin la’akari da takardunsa na ainihi ne, to ya girme min da shekaru bakwai. Babu inda bai sha duka a jikinsa ba sai ka ce ganga. Idan ina tuki, ko’ina rawa ya ke yana girgiza kamar mai rawar nakiya da garma. Shi ya sa idan na yi doguwar tafiya sai na ji jikina kamar wanda aka lakadawa dan karen duka. Ba wannan ne abin damuwa ba, kusan duk tafiyar da nayi ta kilomita biyar sai na tsaya na yi ‘yan gyararraki. Idan kuwa na yi sa’a babu gyara to feshin bakin mai da turnukun hayakin da ke fitowa ta murafunsa sai ya taru ya É“ata min tufafina na yi bakikkirin.

Burina kawai na isa inda aka aike ni na dawo, domin kuwa babu wadataccen mai a tankin. Haka kuma, dazu maburgin ya lalace, baya iya tashi sai an tura shi. Duk na san da wadannan matsaloli, to amma abin day a karu kuma shi ne, ina cikin tafiya na ji babur yana gurnani, yana jan dogon numfashi, yana ajiyar zuciya, yana atishawa. Na hakikance bayan tiya akwai wata caca kenan. Alamu ne na gazawar aikin fulogi. Ba ni da safaya kuwa, ko ina da shi ma na manta sufana a gida. Haka dai na karasa inda aka aike ni yana tutsu kamar sabon jakin da bai samu horo ba tukunna.

Na lalubi birki da nufin na tsaya, nan fa babur ya ce bai san da zaman birki ba. Na shiga kame – kame domin na tsayar da shi daidai lokacin da na doshi wasu mutane da ke zaune kofar ofishin gadan – gadan. Cikin sa’a na shake wuyansa da giya sannan na ware totur kasa. Nan ya ja wani dogon numfashi, wani dunkulen hayaki yayi fitar barden guza ‘fuuuut’ ya bule mutanen nan biyu wadanda tuni sun gama kakatunsu sun zurawa sarautar Allah ido.

Tun kafin na kafe babur din na ke rafka musu sallama, amma suka yi kunnen uwar shegu suka cigaba da hirar su. Da kyar wani ya bude baki ya ce “Yawwa sannu da zuwa.”

Na karasa wurinsu, na farko yana sanye da doguwar riga shudiya mai hasken ruwa da hula dinkin É“arawon damanga wadda ake yi da zaren ulu. Na biyun kuma yana sanye da riga ‘yar shara da hula haÉ“ar kada. Na lura shi ya fi dauke min kai da shan kamshi. A lokaci daya kuma sai na tsinci kai na a mai son lallai sai yayi min magana.

“Sannu baba” Na gaishe shi, ya dube ni da wani irin kallon raini. “Yaya aka yi? Me kake nema anan?” Magana yake yi kamar wanda aka sa masa injin hana magana a baki.
“YallaÉ“ai nake son gani.” Na fada cikin tattausan harshe.
“Daga ina?”
“Daga ma’aikatar yada labarai, fam sek ne ya aiko ni.”
“Me aka aiko ka? Kuma ya san da zuwanka?” Karon farko da na ji hasala na daure ban nuna alama ba.
“Ban sani ba ko ya san da zuwa na, amma sako ne na fatar baki.”
Ya hau guna-guni shi kadai, kamar ba zai ce min wani abu ba. Can ya kalle ni ya ce, “Irinku ne kullum ake maganar ku a rediyo. Ba kwa tuki cikin nutsuwa ga rashin hankali. Ga abin hawan naku ya cancanci a jefar da shi a bola. Yanzu da ka ture mu me za ka ce?” Yayi tsaki, “Nan ofishin mulki ne ba na maula ba, idan wani abu kake nema ka fada mana kawai Malam.” Na harzuka da kalamansa, wato ashe kallon dan maula yake min. Na bude baki zan yi martani, sai ga wata zundumemiyar mota ta danno.

Sautin kida na tashi bugudum – bugudum. Ya gyara motar a wajen fakin. Cikin sauri dattijon nan da ke min bambami ya zabura kamar soja lokacin da aka ba shi umarnin harbi. Ya kama marikin kofar ya bude masa. Wani matashi ya fito sanye da wani dirkeken bakin gilashi da jaket kwat ruwan kasa. Dattijon na gaishe shi amma ko kallonsa bai yi ba, sai amsawa yake ciki-ciki.

Daya mutumin ya dube ni ya ce, “Ka yi hakuri, halin Malam Amadu sai shi, bari ya zo na roke shi ya kai fom din ka. Na amsa da “To madalla na gode.” Nan muka cigaba da hira, anan na nakalci sunansa Labaran, shi kuwa dayan sunansa Amadu.

 

 
Labaran shine maigadi, Amadu shine masinja, amma kankanba da shisshigin Amadu ya kwace duk ayyukan biyun. Ya hana Labaran sakat, ga girman kai ga kushe da sauran munanan dabi’u kamar yadda Labaran ke min korafi. Ni dai na yi zugum ina tunani, har Amadu ya dawo daga maularsa ya zauna. Da sa bakin Labaran ya bani fom din ziyara na cike ya tashi ya shiga. Jimawa kadan ya fito ya kalle ni cikin izza ya ce, “An ce ka shiga.”

Zuciyata na cike da mamakin halin wannan dattijo, shi dai ba wani mai fada a ji ba, ba wani babban ma’aikaci ba amma ya dorawa kansa girman kai fiye da kima. Na tabbata ko yanzu matsayina a aikin gwamnati ya wuce nasa. Domin kuwa mukamin babban direba ne da ni. Wato matakin albashi na bakwai. Shi kuwa mafi kololuwar masinja ko maigadi shine matakin albashi na hudu. Watakila ma shi bai wuce na biyu ko na uku ba.

Na shiga ofishin cikin sallama, wani sanyi ya ratsa tun daga kaina har kafafuna. Sannan kamshi ya doki hancina, kafafuna suka nutse cikin tattausan kilishi, babu shakka ofishin mulki ya fi na direbobi kyau nesa ba kusa ba. A kuryar kofar shigowa daga sama akwai wata tangamemiyar talabijin wadda ke nuna sassa dabam – dabam na ginin ofishin har da kofar shigowa. A fisge na dube ta, Labaran da Amadu na zaune suna kallon hanya. A raina na yi addu’ar Allah ya sa dai ogan bai ga zuwa na da abin da ya faru ba.

Na rusuna ina mai gaisuwa. Abin mamaki sai ya miko min hannu muka gaisa. ‘Wannan mutumin ya fi maigidanmu kirki’ na fada a raina.

“Yayi min waya ya ce kana tafe. Tun dazu ya kamata ka zo, me ka tsaya yi a hanya ne?” Na yi murmushi na ce, “YallaÉ“ai gosulo ga kuma abin hawan nawa sai a hankali.”
“Ina sakon?” Ya fada yayin day a miko hannunsa gare ni.
Na sa hannu na fito da takardun daga aljihun babbar rigata na mika masa.” Ya karÉ“a ya dudduba, sannan ya dube ni ya ce, “Komai yaji, ka fada masa zan yi nazarinsu duk abin da ake ciki zan kira shi.”

Na juya zan tafi ina mai masa sallama. “Ungo wannan ka sha mai.” Tun kafin na karÉ“a na ji murna ta kama ni. Na yi godiya. Na kuma juyawa zan tafi ya sake kirana, “Af, please ka ba wa masinja na wannan ya siyo min kati.” Na karÉ“a na fita. 

Tun ina cikin ofishin nake kulle – kullen abin da zan yiwa Amadu domin na rama girman kan da yayi min. Na tsara na zazzage shi kawai, amma ban yarda da haka ba. Wata zuciyar ta ce na farfada masa miyagun maganganu ko na tuÉ“e mu casu. Wannan shawarar ma na yi watsi da ita. Wata zuciyar kuma ta sukwano ta ce na yi masa nasiha. Kafin na zaÉ“i abin da zan yi masa na fita waje inda suke. Babban fatana kawai babur ya tashi ya maida ni inda na fito. Amma na tabbata sai na goge fulogi kuma sai an tura ni tukunna.

A daidai kofar fitowa daga ofishin wata dabara ta fado min. Na kuduri aniyar fashe fushina akan Amadu kuma na sa shi ya tura min babur, alabarshi daga bisani ayi biyan bashi daddawar kauye, an biya wani a sake daukar wani.

Yayin da na fito cikin sa’a Labaran ba ya wajen, hakan ya yi mini dadi domin nufina zai isa cikin nasara. Cikin fara’a na tsaya daidai inda na hakikance kyamara na kallonmu a gaban Amadu, na cusa hannuna cikin jamfa kamar ina laluben wani abu, jimawa kadan na zaro kudin aiken da ogansu ya ce na bashi, naira dubu hudu na mika masa. Ya karÉ“a da rawar jiki, nan take ya saÉ“i godiya gami da addu’a, hannunsa na rawa ya cusa cikin aljihunsa. Ni dai ban ce masa kanzil ba.

“Na gode Alhaji, Allah ya saka da alheri, Allah ya sa ka fi haka. Allah ya kara nisan kwana.” Ni dai ban amsa ba, don na san abin da na kulla.
“Zan samu aron sifanar fulogi kuwa?” Na ce da Amadu. “Bari a lalubo maka a can.” Ya garzaya da gudu. Nan da nan ya dawo rike da sifana. Shi da kansa ya bude min murfin vespa ya kunce fulogin ya goge min sannan ya mayar.
“A taimaka a tura ni babu maburgi.” Na ce da shi bayan ya gama aikin.
“An gama yallaÉ“ai.” Na dare kan zabuwata, Amadu ya turo ni iyakar karfinsa. Cikin sa’a kuwa ya tashi. Na bashi wuta, duk hayakin ya bule shi amma bai yi ko gezau ba. Yayin da na tabbatar babur ya gama kintsawa, na jefa giya sannan na yafito Amadu da hannu. Ya sheko da gudu. Ya dan rusuna a gabana. Na daga murya saboda karar salansa na ce, “Kudin da na baka, oganka ne yace ka siyo masa katin waya. Ka san yadda ka ke siyo masa!” Ban jira amsar sa ba na murza totur.

Af, ashe na bar baya da kura, na ji ya gundumo min wata annakiyar ashar. Ya jefo ni da wani dirkeken dutse. Nayi sa’a bai same ni ba, amma ya dira akan danjar babur din ta baya. Ta karasa fashewa. Yayin da na yi nisa na taka birki, na juyo har yanzu yana tsaye yana É“aÉ“atu kamar mahaukaci.

Na dora hannayena cikin kunnuwana kamar mai kiran sallah, sannan na dallaro harshena ina masa gwalo. Na lura ni da shi mun soma tara mutane, kila ayi zaton wasu taɓaɓɓu ne sabon kamu. Saboda haka na murza zabuwata nayi gaba ina dariyar shakiyancin da na yi wa wannan talaka mai girman kai. Amma na tabbata haduwar mu ta gaba, karon ba zai yiwa kowa dadi ba tsakanin ni da shi.
Post a Comment (0)