BABU CUTAR DA BABU MAGANINTA ACIKIN ALQUR'ANI 💧



💧🍒

BABU CUTAR DA BABU MAGANINTA ACIKIN ALQUR'ANI 💧

💧Ibnul Qayyim Allah ya masa rahama yana cewa: "Alqur'ani shine cikakken magani ga kowane irin cuta, na zuciya ne ko kuma na gangan jiki ne, cuta ta duniya ko ta lahira, babu wani da zai nemi waraka dashi face ya dace batare da jinkiri ba. 

💧 Idan mara lafiya ya kyautata magani da Alqur'ani, ya rikeshi da gaskiya da imani, ya karbeshi hannu biyu, da quduri nagartacce, sannan ya cika sharrudansa, to wallah babu wani magani kamarsa har abada, tayama za'a samu kamarsa bayan shine maganar Ubangijin sammai da kassai, maganan da idan an saukar dashi akan duwatsu zai narkashi, idan kuma akan kasa aka sauke zai rabata gida biyu, babu wata cuta cikin cututtukan dake damun zuciya da ganganjiki face acikin Alqur'ani akwai hanyar da za'abi wajen maganceta da hanyar rigakafi daga kamuwa da ita, amma kadai Wanda zai gano hakan shine wanda Allah ya azurta da fahimtar littafinsa". 

الطب النبوي ١/٢٦٦

#Zaurenfisabilillah

TELEGRAM:
https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)