MACE TAGARI
-
Mace tagari kalma ce da ko wacce mace take son ta ga ta alaqantu ko an alaqantata dashi ko da kuwa ba ta da abubuwan da za'a ƙirata da ta gari ɗin, domin kalma ce da take mayar da mummunar mace kyakykyawa, ta ɗaga darajarta tare da ƙimantata da ƙara mata farin jini a cikin al’ummar da take rayuwa dasu.
-
Idan ki ka zama mace tagari to kin zama zinariyar da kowa ke son mallaka ko da mijin ki ne ya rasu, ko yayi kuskuren rabuwa da ke, to kowa zai ta rububin son auren ki Saboda kasancewar ki tagari, za ki zama abun kwatance ga ƙawayen ki da ƴan’uwan ki kuma abun buga misali a wurin salihan mutane Sannan ki mutu ki shiga Aljannah madaukakiya.
-
Telegram
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
-
Instagram
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5
