Babu Bambanci Tsakanin Dan Zina Da Dan Halal A Wajen Rabon Gado !



Babu Bambanci Tsakanin Dan Zina Da Dan Halal A Wajen Rabon Gado ! 
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamualaikum dan Allah tambaya nake yi mu biyar mamanmu ta haifa amma biyu daga cikinmu ta hanyan aure aka same su uku kuma ba tahanyar aure aka same su ba, shin sunada gadon ta ko, ba su ? kuma ta mutu da bashi da yawa akanta kuma ba mu da hanyar biya mata shi domin kuÉ—in suna da yawa akalla yakai dubu dari biyu.
Dan Allah mafita muke nema, Mungode
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikum assalam, idan mace ta yi cikin shege kuma ta haifi ÆŠa, daga baya ta mutu ÆŠan zinar da ta haifa zai gaje ta, saboda Allah madaukakin sarki a cikin suratun Nisa'i aya ta : 10 ya yi wasiyya a bawa 'ya'yaye gado, ÆŠan zina kuma yana cikin jerin 'ya'yayen mahaifiyarsa, wannan yasa zai gaje ta.                                                                                                                                                               
Don haka babu Bambanci a cikinku tsakanin Wanda aka haifa ta hanyar aure da kuma Wanda aka samu ta hanyar Zina.
Ba'a raba gado sai an fara biyawa mamaci bashinsa, don haka ko da duk abin da ta bari zai kare dole Ku biya kafin a raba, kamar yadda Allah ya bayyana a cikin suratun Nisa'i aya ta (11).

ÆŠan zina baya gadon mahaifinsa ko da kuwa mahaifin ya amince ÆŠansa ne a wajan mafi yawan malamai.

Allah ne mafi sani.

*Dr. Jamilu Zarewa*

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

_Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING wasu da yawa zasu amfana._
Post a Comment (0)