HUKUNCIN WUCEWA TA GABAN MAI SALLAH?



HUKUNCIN WUCEWA TA GABAN MAI SALLAH?
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum. Malam akwai iyaka game da tazara ta yadda mutum zai iya wuce ta gaban mai sallah ? . Jazaakallahu khairaa.
:
*AMSA*👇
:
Walaikumus salamam Warahmatalahi wabarkatahu

Sanya Sutura ita ce wani abu da mai sallah zai sanya a gaban shi, tsakaninsa da wanda zai wuce ta gaban shi.

Sanya Sitira wajibi ne, saboda Manzon Allah ﷺ ya yi umarni da sanya sitira ga liman da wanda yake shi kaɗai, ya kwadaitar akan yin hakan, don haka ya kamata musulmi ya sanya sitira a gabansa yayin da zai yi sallah, ya hana wanda zai wuce tsakaninsa da tsakanin sitirarsa, saboda fadin Manzon Allah ﷺ “Kada ka yi sallah sai da sitira, kada ka bar wani ya wuce ta gabanka, idan ya qiya ka hana shi”[Ibnu Khuzaima ne ya rawaito shi]

Manzon Allah ﷺ ya ce, “Idan dayanku ya tashi yana sallah, idan a gabansa akwai (sitira) kwatankwacin sandar dake qarshen sirdin raqumi to tana yi masa sitira (ta kare shi). Idan kuwa babu kwatankwacin sardar dake qarshen sirdin raqumi a gabansa, to (wucewar) jaki da mace da baqin kare suna yanke masa sallah “Yace, nace,” Ya Abu Zarrin! Me yasa kare baqi (kawai) daga cikin karnuka ruwan dorawa? Sai ya ce, “Ya ɗan Ɗan'uwana, na tambayi Manzon Allah ﷺ kamar yadda ka tambaye ni, sai ya ce min, “Baqin kare shaidan ne”[Muslim ne ya rawaito shi].

Wucewa ta gaban mai sallah baya halatta, yana ma cikin manya-manyan zunubai, saboda faɗin Manzon Allah ﷺ “Da wanda yake wuce wa ta gaban mai sallah ya san abin da yake kansa (na laifi) da ya tsaya arba’in shi ya fi masa alheri a kan ya wuce ta gaban (mai sallah). Abun Nadri “mai riwayar hadisin” ya ce, : “Ban Sani ba, kwana arba’in ya ce, ko wata ko shekara?” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

(Babu laifi) idan wucewar ta bayan sitirarsa ce, ko kuma ya wuce nesa da shi, daga bayan wurin da yake sujjada idan shi mai sallar bai sanya sitira ba.

Dole ne akan mai sallah ya hana wanda zai wuce ta gabansa.

An karbo daga Abu Sa’id – Allah ya yarda da shi – ya ce, na ji Manzon Allah ﷺ yana cewa, “Idan dayanku yana sallah da wani abu da ya kare shi daga mutane (Sitira), sai wani ya yi nufin ya wuce ta gabansa, to ya tunkude shi, idan ya qiya to ya yaqe shi, domin shi Shaidan ne”[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Tazarar da take tsakanin mai sallah da sitira ana qaddara ta da kwatankwacin wurin da akuya zata iya ficewa, saboda hadisin Sahli – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Tsakanin wurin sallar Manzon Allah ﷺ da sitirarsa, akwai kwatankwacin wurin da akuya zata iya wuce wa”[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Wallahu A'alamu

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)