YA HALATTA NA SAKI MATATA SABODA TANA DA CUTAR HIV/AIDS ?

YA HALATTA NA SAKI MATATA SABODA TANA DA CUTAR HIV/AIDS ?


*TAMBAYA*❓
:
Malam matata ta yi rashin lafiya, da aka gwada ta, sai aka ce tana da cutar aids, ni kuma an gwada ni amma an ce bani da ita, Sannan an gwada ragowar matana, suma an samu ba su da ita, gaskiya malam ina so zan sake ta, saboda kar ta shafe mu, amma ina neman shawara ?
:
*AMSA*👇
:
To dan'uwa cutar aids tana daga cikin cututtuka sababbi, wadanda ba'a tattauna su ba a manyan kundayen musulunci, saidai idan muka duba manufar da ta sa aka shar'anta saki wato tunkude cuta da matsala, daga ɗaya daga cikin ma'aurata ko su duka, za muga ta tabbata a wannan cuta, tun da ilimin likitanci ya tabbatar da cewa cuta ce mai haɗari kuma ana daukarta, don haka ya halatta ka sake ta, saboda wannan dalilin, tun da malaman Fiqhu sun halatta raba aure saboda cutar kuturta, kamar yadda hakan ya zo a Minahul Jalil Sharhu Muktasarul Khalil : 6\478 Cutar Sida kuma tafi kuturta tsanani. Sannan ba za'a kalli cutuwar da za ta yi ba, bayan an saketa, domin yana daga cikin ka'idojin Sharia : kau da kai daga tunkude cutar da za ta shafi wani saboda cutar da za ta game, Cigaba da zama da ita zai jawo ka dauki cutar, kuma iyalanka su dauka, wannan yasa ba za'a waiga zuwa damuwarta ba a nan wurin. 

Allah ne mafi sani.

Jamilu Zarewa

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)