ƊAYA BISA UKUN DARE NA ƘARSHE!
Daga Sahabi Abi Huraira Allah Ta'ala ya yarda da shi ya ce, Lallai Manzon Allah saw ya ce; Ubangiji yana saukowa mai girma da daukaka a kowani dare zuwa saman duniya, a sanda ya yi saura daya bisa ukun dare na 'karshe , yana cewa, Wa zai kirani in amsa mishi, wanene zai rok'eni in bashi, wanene zai nemi gafarana ni kuma in gafarta masa.
{Imam Bukhari da Muslim, Dariqus-salihin, 58p.
.
Wanda duk ya takaita baccinsa, ya dage da sallan dare don Neman yardan Allah, da sannu zai 'kara samun kusanci ga Allah, da kuma biyan bukatunsa na duniya da lahira.
Allah ya sa mu dace.
Zaurenfisabilillah
Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah