DUNIYAR MUTUWA //01

DUNIYAR MUTUWA //01




A daya daga cikin tadfiye tafiye na
zuwa Birnin Riyaad, nai shirin zuwa
filin jirgin sama kafin lokacin tashin
Jirgin da Awa 1, sai dai cunkoson
hanyar, da kuma Bincike yasa na
makara a tafiyata, sai na dinga
sauri har na isa wajen tsayuwar
motoci, sai na dauki Kaati na (Visa)
da sauri, nai Parking motata a
wurinda ni bansan shin wurin
Parking din ma'aikata ne ko na
matafiya, ni dai na sauko da sauri
daga mota na dauki Jakaata a
hannuna, na shiga abin tafiya
(Escalator) na isa dakin bincike, na
cire duk abindake aljihuna na riqe a
hannu, na danna na'urar bude qofa,
amma sai naji sanarwar cewa wai a
jikina akwai wani abu da bazan iya
wucewa dashi ba, sai na shiga
damuwa, chan sai na tuna Agogona
ne ai, sai na cire, na sake danna
na'urar, sai ta bude na wuce lafiya.
Na isa wajen mai bada Tikitin Jirgi
da sauri, nace: Ni matafiyi ne zuwa
Riyaad, cikin jirgi mai lamba 1411,
sai ma'aikacin yace: Ai Jirgin ya cika,
sai nace dashi: Don Allah ka
taimakamin, inada Alqawarine
wanda ba makawa in halarceshi a
wannan Dare.
Sai yace: Kada ka yawaita magana,
don Jirgi ya riga ya cika, kuma babu
wanda zai daga maka qafa, sai
nace: Hasbiyallah!!!!
Na fito daga wajensa, na tsaya ina
kallon jirgin banida tsimi banida
dabaarah face ga Allah, sai tunani
yadinga ketomin akaina cikin sauri!
Shin zan bar tafiyar nan ne? Kodai
in tafi a Motata? Ko in dauki hayar
mota in tafi? Sai dai zuciyata ta
bani in tafi a motar haya, sai na
koma bangaren yan Tasi (Taxi), sai
na samu wani mutum cikin
sabuwar Mota (Camry), na ce dashi:
Nawa zaka kaini Riyaad? Yace:
Riyal 500! Nayi qoqarin samun ragi
wajensa, amma bai ragen komaiba
illa Riyal 50.
Na hau Motar ni kadai, nace dashi
yayi sauri, domin dolene na Isa
Riyaad cikin wannan Dare, ni ban
sani ba, ashe qarshena cikin Awanni
ne!!!!!!!!
Yace dani: Sha Kuruminka, zanyi
gudu dakai tamkar Tsuntsu, ai
kuwa haka akai, ya dinga gudu na
hauka, don na masa Alqawarin idan
ya isa Riyaad dani kafin Isha'I, zan
bashi qarin kyautar Riyal 100
(bayaga 450 dinsa).
Muna tafe muna hira yana
tambayata ina tambayarsa muna
raha, don dai mu debe kewar juna!
Kwatsam sai mahaifiyata ta
fadomin qwaqwalwata akan in
kiraata, ai kuwa na kirata, tace: Ina
kake ne ya Aba-Saarah?
Sai na bata Labarin Jirgi, da yanda
na rasa tafiya ta Jirgi, sannan yanzu
na hau mota ne don tafiyar, sai
tayyi shiru, wanda hakan ya janyo
hankali na, sai mhaifiyata tace: Ka
kula ya kai Daana, Allah kareka
daga sharrin abindake boye, sai
nace: Amin, zan kiraaki da zaarar na
isa Inshaa Allah, kinada wasiyya
gareni ne? Tace: kasancewarka
Lafiya ya Tsayin Rayuwata!!!!!!. .......
Anan muka kammala waya da ita!
Sai naji wani abu a raina, nakejin
wani abin Al-ajabi na shirin
Aukuwa dani! Sai na kira Mataata,
tace: Bani Labarinka ya rayuwata,
Kilomita nawa kukai? Nace: Yanzu
munyi Kilomita 150. Tace: Wallahi
munyi rashinka, in baka gidannan
duk babu dadi! Nace: Allah ya maki
Albarka, in Allah yaso inanan
dawowa a jirgin Raana, ki kula da
yaara na, ki sumbancemin Susu,
Allah ya kula mana da ita! Tace:
albishirinka, ai tun randa ta dawo
take ina Baba? Nace: Bani ita! Susu
tace: Baba ina kake? Nace: Susu nan
bada jimawa ba zan dawo maku
inshaa Allah, muka danyi dariya
nace to ba Mama wayar, sai ta bata,
nace: kinada wata wasiyyace
gareni? Tace: Fataana shine
kubutar rayuwarka! Ban sani ba
menene dalilinda yasa damuwa ta
soma tsananta agreni! Na shiga
Zurfin tunani wanda ban dawo ba
sai ji nayi Direba na
Tambayata...... ...............
Ko me Direban ya Tambayeshi?
Shin ya zasu qarke a hanya, yana
isa Riyaad kuwa????
Mu hadu zuwa anjima domin jin
kashi na biyu.

Zamu chigaba da yardar Allah ....

 #Adam sani Abu umayra

Daga
*miftahul ilmi*

Zaku iya bibiyar mu 

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)