ANNABI DA SAHABBANSA // 082


ANNABI DA SAHABBANSA // 082
.
Mawallafi: Baban Manar Alqasim
.
AN RUFE SHAHIDAN UHUD
Yaqi ya qare, kuma kowa ya binciko gawarsa, wasu ma har sun riga sun shigar da tasu Madina, sai Annabi SAW ya yi umurni da a dawo da gawawwakin don a burne su a Uhud, haka ya ce a rufe su ba tare da an yi musu wanka ba, duk suna cikin suturunsu, kayan fata da na qarfe ne kawai aka cire, wato sulakensu, sai aka riqa hada mutum 2 a sutura daya a rufe su tare a qabari guda, kawai dai Annabi SAW yakan tambaya ne wa ya fi haddar Qur'ani a ciki, in an nuna masa sai ya tura shi cikin lahadi.
.
Annabi SAW ya sanya su a qaburburansu yana cewa "Ni ne shedarsu a ranar qiyama" ya hada Abdullah bn Amr bn Haraam da Amr bnl Jumuh a qabari guda, don ko tun suna da rai abokan juna ne masoya (Buhari 2/584), a ka nemo gawar Hanzala, can sai aka same shi yana zuban ruwa, Annabi SAW ya ce mala'iku ne suke wanke shi, daga nan ne aka tambayi iyalinsa, shi ne ta fadi halin da yake ciki ya bari ya fita jihadi, tun daga nan ne ake masa laqabi da wanda mala'iku suka wanke (Zadul Mi'aad 2/94)
.
Hamza RA in mun tuna ba baffan Annabi SAW ba ne kacal, dan uwansa ne, don sun ma sha nono guda da shi, ka ga in 'yan Shi'a da gaske suke yi, shi ya kamata su fara kawowa a matakin farko, amma da yake wanda ya kashe shi bai cancanci a tsine masa ba, ko kadan Annabi SAW da sauran ahlul baiti ba su sunnanta tsinarsa ba, in har Annabi SAW ya jima yana jin radadin mutuwa to ya ji ta baffansa, kisansa tabbas ta tabi zuciyar Annabi SAW, babarsa Safiyya ta zo don duba dan uwanta amma Annabi SAW ya sa danta Zubair ya maida ta gida, ta tambayi dalili.
.
Ta ce "Ai na riga na sami labarin an illata gawarsa, na san wannan a tafarkin Allah ne, zan haqura na dangana in sha Allah, da ta zo ta gan shi ta yi Inna-lilla, ta nema masa gafara ta yi masa addu'a, Annabi SAW ya sa aka rufe shi tare da Abdullah bn Jahash, sun sha nono tare kuma dan 'yar uwarsa ne, jikin sahabbai duk ya mutu, Khabbaab ya ce "Ba a ma sami likkafanin da za a rufe shi da shi ba sai wani qyalle wanda in an ja ta wurin kan qafa ta fito, haka aka sa wani ganye a sauran wurin qafafun"
.
To bayan burne mamatan ne gaba daya sai Annabi SAW ya koma Madina tare da sahabbansa cikin murna da farin ciki, a kan hanyarsa ce ta komawa ya hadu da Hamnah bnt Jahash ya yi mata ta'aziyyar dan uwanta Abdullah bn Jahash, da kawunta Hamza bn Abdilmuttalib ta yi inna lillahi ta nema musu gafara amma da ya gaya mata ta mijinta Mus'ab bn Umair sai ta daga murya ta rangada guda, Annabi SAW ya ce "Mijin mace na da matsayi a wurinta" Ibn Hisham 2/98
.
A qarshe dai Annabi SAW ya isa Madina a ranar Asabar 7 ga watan Shawwal shekara ta 3 Hijiriyya 07/10/0003, mafi yawancin littafan tarihi sun tafi ne a kan cewa sahabbai 70 suka yi shahada, kuma galibinsu Ansarawa ne, an kashe musu mutum 65, 41 Khazrajawa ne, 24 kuma Ausawa sai Bayahude qwara daya tal, shi ma dai daga nan din ne, a Muhajirai kuwa mutum 4 ne kacal suka yi shahada.
.
Mushrikai kuwa Allah SW cikin ikonsa mutum 24 ne kawai suka baqunci lahira, amma in aka duba sosai a Ibn Hisham a wurare da dama, da Fat'hul Bari 7/351, da Gazwatu Uhud Muhammad Ahmad p278-280 za a taras mamatansu sun kai 37, musulmai sun koma Madina a daren Lahadi a gajiye amma tare da shirin ko-ta-kana, an zuba matakan tsaro a ko'ina kuma Annabi SAW shi ne kwamandan da kansa.
.
YAQIN HAMRAA'UL ASAD
Annabi SAW dai ya kwana yana ta nazarin yaqin, yana ganin in har mushrikai suka ga nasara da rinjayen da suke ganin sun samu kuma hakan bai dada musu komai ba tabbas za su iya yin nadamar hakan su kuma juyowa da baya su yaqi Madina, don haka ya tsaya kan yadda za a yi musu rakiya, gari na wayewa, wato bayan Uhud da kwana daya Lahadi kenan 8 ga watan Shawwal shekara ta 3 Hijiriyya ya miqe cikin sahabbai RA ya kwadaitar da su yaqi sannan ya yi umurni da kar wani ya bi su in ba wanda aka fita Uhud tare da shi tun farko ba.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)