KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 11

KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 11



Mawallafi: Sheikh Aliyu Said Gamawa
.
ABUBUWAN DA SABABBIN KAFOFIN SADARWA NA ZAMANI SUKA TANADA
Alal haƙiƙa kafofin sada zumunta na zamani sun zo da gagarumin canje-canje a salon zamantakewar bil'adama baki ɗaya. Babu wani sashi na rayuwar ɗan'adam da wannan canji bai shafa ba, kama daga addininsa, mu'amalar iyali, kasuwanci, zamantakewar yau da kullum har zuwa shugabancin al'umma.
.
Sabuwar fasahar sada zumunta ta tattara wasu muhimman al'amura waɗanda duniyar sadarwa ba taɓa kai wa zuwa gare su ba. Irin waɗannan al'amura sun haɗa da:
1. Fasahar sada zumunta ta zamani ta samar da damar isar da saƙonni kai tsaye ta hanyar na'ura ba tare da shamaki ko iyakancewa ba.
.
2. Wannan sabuwar fasahar ta ba da damar aika saƙo da musayar yawu a tsakanin mutane biyu ko wasu gungun mutane a cikin sirri ba tare da sauran jama'a sun san abin da ke gudana ba.
3. Wannan fasaha ta buɗe wata ƙofa da mutane ke aika saƙonni kai tsaye ga duniya ta hanyar da kowa zai iya gani, kamar yadda suke buƙata ba tare da iyakancewar wani ba, kuma nan take ya isa ga duniya kai tsaye batare da ɓata lokaci ba.
.
4. Wannan fasaha ta samar da yanayin da mutane ke iya aika kowane irin saƙon hoto ko bidiyo na abubuwan da duk suke so, a lokacin da abubuwan ke gudana ko kuma bayan sun tantance ainihin abin da suke buƙatar mutane su gani, gwargwadon manufar aika su.
5. A ƙarƙashin wannan fasaha mutane kan iya tsintar wani saƙo a yanar gizo ba tare da sanin wanda ya wallafa shi ko kuma tantance sahihancin bayanan da ke cikinsa ba, sannan sai su sake yaɗa shi ta hanyar turashi ga waninsu, ta haka har saƙon ya mamaye duniya ba tare da ma an san haƙiƙanin wurin da ya fito ba.
.
6. Wannan sabuwar fasahar ta na ƙulla zumunta tsakanin mutane daban-daban a sassan duniya, kuma a rukunin rayuwa daban-daban ba tare da gindaya wani ƙari ba. Sannan kuma ga wata dama ta ƙulla abota babu shamaki tsakanin rukunin jama'a iri-iri. Kamar misalin yadda ake ƙulla abotar musayar ra'ayi da mahawara tsakanin ƴaƴa da iyayensu ko tsakanin malamai da ɗalibai ko tsakanin ƙwararru da gama garin jama'a ko tsakanin abokai ko alaƙar saye da sayarwa da sauransu.
.
Bisa la'akari da waɗannan muhimman sauye-sauye da kafofin sada zumunta na zamani suka kawo a fagen mu'amalar bil'adama, za mu iya cewa duniyar sadarwa ta samu muhimmin ci gaba, wanda tunani da hasashen ɗan'adam bai taɓa tsammanin su a can baya ba. Wasu daga cikin irin alfanun da wannan gagarumin ci gaban fasahar sadarwa ta kawo sun haɗa da:
.
i. Fasahar kafofin sada zumunta na zamani tana ba da damar isar da saƙonni ga jama'ar duniya kai tsaye ba tare da la'akari da nahiyar da mutum ya fito ba, ba kuma tare da nuna bambancin jinsi ko matsayi tsakanin mutane ba. Babu wani lokaci da aka samu wata kafa wadda ta hanyarta ake iya kai wa ga dukkan mutanen duniya kai tsaye babu ƙaidi fiye da wannan zamani na amfani da fasahar sada zumunta. Ta hanyar waɗannan kafofi an samu damar cuɗanya da musayar bayanai tsakanin dukkan rukunan ɗan'adam ba tare da la'akari da bambancin shekaru, nahiya, jinsi ko matsayi da matakan rayuwa ba.
.
ii. Fasahar kafofin sada zumunta na zamani ta sauƙaƙa yadda ake isar da saƙonni tsakanin mutane a wajen kai wa ga jama'a a cikin gaggawa ba tare da ɗaukan lokaci ba. Haka kuma ta sauƙaƙawa jama'a isar da saƙonni ba tare da an kashe kuɗaɗe masu yawa ba, ta kawo sauƙi matuƙa wajen ba da manufa ko aƙidar rayuwa ga duk wani bayani ko wata manufa ko aƙidar rayuwa da aka yaɗa wa duniya, kuma ta kasance marar sahihanci ko mai illa ga addini da zamantakewar bil'adama.
.
iii. Fasahar kafofin sada zumunta na zamani ta samar da yanayin da za a iya tattara ilmi wuri guda ta hanyar wallafa littattafai, ƙasidu da sauran rubututattun bayanai masu ɗumbin yawa, kuma a yaɗa su kai tsaye su isa ga mutanen duniya baki ɗaya a cikin ƙiftawa da bismillah. Babu wani lokaci da duniya ta samu gatan tattara rubutattun saƙonni masu yawan gaske wuri guda tare da iya yaɗa su ga jama'a masu ɗumbin yawa nan take, fiye da wannan lokaci.
.
iv. Fasahar kafofin sada zumunta na zamani ta ba da damar sarrafa saƙonni cikin murya da hotuna, waɗanda aka naɗa a faifai kuma aka yi tanadin hotunansu ko kuma waɗanda ake gabatarwa kai tsaye, sannan a aika ga ɗaukacin duniya don duk mai buƙata ya saurara ko ya gani da idanuwansa. Wannan muhimmiyar dama ce da duniya ba ta taɓa hasashen ta ba ko a mafarki. Hanya ce da wasu mutane suka yi nisa wajen amfani da ita don yaɗa manufofi da aƙidojin addininsu, salon zamantakewa da rayuwarsu don duniya ta raja'a gare su, amma abin ƙarfafa gwiwa a nan shi ne, babu wani shinge da aka sanya don a hana kowa yaɗa manufarsa ko addininsa, sai dai wanda halin biris, lalace da rashin kishi ko ɗaukan al'amuransu da muhimmanci suka yi wa tarnaƙi.
.
v. Fasahar sada zumunta ta zamani ta kawo canji matuƙa tare da sauƙaƙe hanyoyin ba da ilmi, kiwon lafiya da kasuwanci. Akwai ƙofofi masu yawa da aka buɗe a ƙarƙashin waɗannan kafofi don yaɗa ilmi da wayar da kan jama'a a dukkan fagagen rayuwa, kama daga ilmin addini, sana'a, zamantakewa da mu'amalolin ɗan'adam.
vi. Fasahar sada zumunta ta zamani ta samar da hanyoyin ba da kariya ga masu rauni ta hanyar takawa azzalumai birki da kuma sanya masu kula da da al'amuran jama'a su kasance a cikin taka-tsantsan wajen gudanar da ayyukansu.


.

Rubutawa:- Shaikh Aliyu sa'id Gamawa
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi


Post a Comment (0)