LABARI »»» 01

LABARI »»» 01



AN BAR MASA KOFA A BUDE

Yana da matarsa da ya’yansa, amma ga shi yau ya shafe kwanaki ko kifi daya ba ya kamowa idan ya tafi su, ga shi ba wata sana’a da ya iya ga iyalinsa cikin tsananin yunwa. Ga shi yau ma har yamma babu alamar samun wani abu, ya daga calinsa ya ce: “Wannan ne na karshe, idan ban kama komai ba sai in dogara ga Allah in tafi gida”. 

Allah Buwayi, sai ya kama wani katon kifi, katon gaske, a duk shekarun da ya yi bai taba kama kamarsa ba. Kawai sai ya nutsa kogin tunani, yana cewa zai bai wa ‘ya’yansa wani, ya raba wa makwabta wani daga ciki, sannan ya sayar da wani bangare daga cikinsa, sai ya ji ana cewa: “Kai kawo wannan kifin, sarki ya ce a kai masa, domin ya ba shi sha’awa”.  

Sai mutumin ya firgita, ya tuna ‘ya’yansa da matansa cikin yunwa, sai kawai ya tubure, ya ce ko dai a biya shi kudin kifinsa, ko kuma ba zai bayar ba. Sarki ya ce babu wani abu da za a ba shi, domin komai mallakin sarki ne. Haka aka kwace, aka dafe wa sarki ya cinye. 
Ba a juma ba sai sarki ya kamu da ciwon daji (cancer) a kafarsa, sai likitoci suka ce, ai lallai sai an gutsure dan yatsan kafar. Sarki ya ki, aka nemo wani likita daga wani gari. Ya ce sai an yanke sawunsa gaba daya, sai sarki ya ki. Aka sake nemo wani likitan sai ya ce: Ai sai an yanke har zuwa gwiwar kafa domin ciwon ya hau har zuwa nan, idan kuma ba a yi haka ba, to lallai zai hallaka sarki. 

Haka aka yanke kafar sarki. 
Yana cikin jinya, sai ya sami labari ‘yan tawaye sun bayyana suna neman sai an kawar da shi daga karagar mulki. Hankalinsa ya tashi, nan take aka nemo babban malamin garin don abin kuma ya zama abin ban mamaki. 
Babban Malam ya tambayi sarki ko ya zalunci wani? , sai sarki ya yi iya tunaninsa ya ce shi bai san ya zalunci wani ba. Sai Malam ya sake cewa: Lallai dai a zurfafa tunani, domin irin wannan al’amari zalunci ne yake kawo shi. Kamar walkiya sai ya tuno masuncin nan. 

Sarki ya tura fadawa suka fita aka same shi kuwa a bakin teku yana su. Sarki ya tambaye shi, ya ce: “Me ka yi lokacin da muka kwace maka kifinka”. Cikin firgici sai masuncin nan ya ce: “Ni ba abin da na yi”. Sai sarki ya sake maimaitawa shi ma ya sake maimaita amsarsa. Sai sarki ya ce: “Na baka aminci, babu abin da zai same, ina yi maka magiya me ka yi?”. Sai masuncin nan ya ce: “Na daga hannayena ga Allah na ce: Allah Ka ga yadda ya nuna mini karfinsa a kaina, Allah Ka nuna mini karfinKa a kansa”. 

Manzon Allah (SAW) ya ce wa Mu’az dan Jabal: “Ka kiyayi addu’ar wanda aka zalunce shi, domin babu hijabi tsakaninta da Allah”. Tirmizi.

Dr, Abdulkadir Isma'il 

Daga 
MIFTAHUL ILMI

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)