SHIN YA HALATTA HADA LAYYA DA AQIQA?

SHIN YA HALATTA HADA LAYYA DA AQIQA?

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

AMSA:

Idan layya da aqiqa suka hadu, kanaso kaiwa danka yanka ranar idin babbar Sallah, ko aranakun gyaran nama, shin layya ta wadatar maka da yin aqiqa?.

Malamai Sunyi Zantuka guda biyu akan wannan Matsalar.

Nafarko, layya bata iyuwa ahadata da aqiqa, wannan shine mazhabar malikiyyah da shafi'iyyah da ruwaya daka imamu Ahmad.

Hujjarsu itace: ko wanne daya daka cikinsu karan kansa yake ci, tsakanin layya da aqiqa,

Daya bata wadatarwa akan daya, kowanne cikinsu yana da Sababinsa, sababin kowanne ya saba dana dayan, daya bata tsayuwa da daya.

Kamar yankan tamattu'i da yankan fidya.

Haitamy rahimahullahu acikin Sharhin Minhaaj (9/371) yace:  Idan mutum ya niyyaci yankan aqiqa da layya da dabba daya bata wadatar akan dayar ba, wannan shine zahiri, domin kowanne acikinsu sunnace mai zaman kanta.

Zance Na biyu: Layya tana wadatarwa akan aqiqa,  ruwaya daka Imamu Ahmad itace mazhabar Ah-naaf, haka hasanul basary da Muhammad bin Sireen da Qatada Allah yajiqansu da rahama Sukace

Hujjarsu itace: Dukkansu manufar yinsu shine samun kusanci zuwa ga Allah da yanka, daya tana shiga cikin daya, kamar yanda tahiyatul Masjida take shiga cikin Sallar farillah ga Wanda ya shiga masallaci.

Al-Musannaf na Ibnu Abiy shaiba (5/534).

Hasanul Basary yace: idan kaiwa yaro layya ta isar masa akan aqiqarsa..

Kamar yanda Shishaam da Ibnu sireen sukace

Qatada yace: Layya bata wadatarwa akan aqiqa, harsai anyi masa aqiqarsa.

Buhty acikin sharhin muntahal iradaa (1/617) yace: idan lokacin aqiqa yai dai-dai da lokacin layya, idan akai aqiqa ta wadatar akan layya, idan akai layya ya wadatar akan aqiqa..

Kamar juma'a ce tayi dai-dai da ranar idi, idan kai wanka daya ya isar akan dayan, haka wanda yai yanka saboda tamattu'i ranar Sallah, ya isar masa akan layyah.

Kamar yanda yazo acikin kashshaful Qina'i (3/30).

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai

. WhatsApp Group

2348123432272

Post a Comment (0)