TARIHIN HAMSHAKIN MATAFIYI IBN BATTUTA Kashi na Uku.

TARIHIN HAMSHAKIN MATAFIYI IBN BATTUTA
Kashi na Uku.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
Bayan Ibn Battuta ya kammala aikin Hajjinsa, sai kuma ya É—aura harami ya shiga cikin wani ayari mai tafiya kasar Iraqi. Daga can kuma bayan ya huta sai ya wuce zuwa Iran, a inda babu jimawa ya sake tattaro kayansa ya biyo ayarin mahajjata, sai gashi a saudiyya.
Daga nan bai zame ko ina ba sai gabashin afirka, inda yayi kara-kaina, ya zagaya kasashen larabawa ta kudu, sannan ya sake É“ulla kasar saudiyya.
A wannan karon ma bai jimaba, sai yabi tawagar wasu matafiya, kwanci tashi sai gashi a Misira. Ya sauka yayi 'yan kwanaki, sannan ya tashi izuwa kasar syria, a inda babu jimawa ya tsallaka babban teku ya dira a Crimea.
Anan ne kuma tafiyar Ibn Battuta ta mika izuwa yankin Asia, inda ya shiga kasashen Khwarizm, Bukhara da Afghanistan, sannan ya tsallaka tsohuwar daular musulunci data kafu a Delhi É—in kasar India.
Ibn Battuta ya shafe shekaru biyu a Delhi yana rike da mukamin alkalin alkalai. Daga nan yaji tawaga zata tashi zuwa birnin Sin (China), cikin azama yace zai bita.
Akan hanyarsa ta zuwa china ya sauka a Maldives har ma yayi aikin alkalanci na watanni shidda, sannan ya cigaba izuwa Ceylon, Bengal, Zaitun da Canton, har dai a karshe ya riski china.
Ance a farkon shekara ta 748 hijiriyya, Ibn Battuta ya sake É—aura É—amarar komawa kasashen Iran, Iraq da syria, daga bisani kuma sai ya koma saudiyya domin sake gabatar da aikin Hajji.
Bayan ya kammala sai kuma yabi ayarin wasu libiyawa ya riski garin Fezzan mai makotaka da Borno, sannan ba tare da gajiyawa ba kai tsaye yayi haramar tun karar garin Grenada na kasar spain.
Daga can ne kuma sai ya sake É—aura sirdi, ya dawo yankinmu na afirka, inda kai tsaye ya tunkari birnin Timbuktu na kasar Mali, sannan ya garzaya izuwa garin Gao, daga nan kuma labarnsa ya riske kasarsu Morocco, sai Sultan Abu Inan ya aika masa ya dawo gida.
Bayan Ibn Battuta ya koma gida ne ya labartawa sakataren fadar sarkin kasarsu mai suna Ibn Djozay duk labarin tafiyarsa, wanda shine aka taskance tare da maidashi littafi mai suna RIHLA.
A karshe, Ibn Battuta ya rasu a kasarsa ta haihuwa a shekarar 1368 zuwa 1369.
Littafin Rihla kuwa na É—aukene da labarin tafiyar Ibn Battuta tun daga sanda yabar garinsu Tangier har sanda ya komo, da yadda yasha wahalar tafiya gami da yadda ya rinka samun arziki yana kuma kyautar dashi ga mabukata.
Haka kuma Ibn Battuta ya bayyana mummunan labarin abin daya auku a gareshi yayin haɗuwarsa da wasu 'yan fashin teku a yankin Turai, waɗanda suka tsareshi tsawon kwanaki takwas tare da kwace dukiyarsa, a karshe da kyar ya kuɓuta daga hannunsu daga shi sai dardumar sallah. Amma kuma bayan ya tsallaka garin Malabar ya nemi mafaka, sai aka naɗa shi alkali mai daraja a garin.
Ibn Battuta ya rinka bada hujja a duk garin daya ziyarta, yana mai faÉ—in yadda ya samu garin, ko kuma wani muhimmin abu daya auku a lokacin zuwansa.
Misali
Ya faÉ—a akan zuwansa Kasar saudiyya cewa "Na shafe shekaru biyu ina rayuwa ta tsarki da imani mafi soyuwa ga ubangiji. A koda yaushe ina kusa da ka'aba wajen bautar Allah, da sauran wurare tsarkaka."
Ya faÉ—a akan zuwan sa Cairo cewa "A garin zaka samu manyan masana da jahilai, zaka samu masu gina gumaka da masu bautar ubangiji, masu zafin zuciya da masu karimci.. Cikar garin da batsewarsa kuwa takai ka misaltata da kaÉ—awar igiyar teku. Haka kuma duk da garin tsoho ne, amma gine ginen sa na zamani ne".
Ga kuma abin daya faÉ—a a zuwansa Ceylon "Mutanen cikin birnin mabiya addinin Bhudda ne, amma suna girmama musilmai ta yadda suna basu muhalli da abinci mai daÉ—i."
Amma game da indiyawa, ya faɗa cewar basa taɓa yin abota da musulmi, ba kuma sa bashi abinci ko abinsha, amma basa cutar dashi yayin da yazo wucewa ta kasarsu.
A Zuwansa Turkey, Ibn Battuta ya faɗa cewa Turkawa suna barin dabɓobinsu suyi kiwo babu mai kula dasu, domin dokarsu akan sata mai tsauri ce.
A cewarsa, idan aka samu mutum da dokin sata a Turkey, za'a tilasta shi ya maida dokin tare da karin dawakai guda tara. Idan kuwa ya gaza yin haka, to É—ansa za'a kwace amaimako.
A game da zuwansa china, Ibn Battuta ya faÉ—i cewar yasha mamaki matuka musamaman yadda yaga kaji da zakaru a china manya manya. Har ma yace akwai sanda abokinsa ya siyi kaza don suci, amma saboda girmanta sai a tukwane biyu suka dafa ta.
Haka kuma, Ibn Battuta yace ya kayatu sosai da tulin jiragen ruwa dake gaɓoɓin tekunan kasar china. Ya kuma faɗa cewa a kowacce gaɓar teku, akwai mutum dubu goma masu bada kariya, ɗari shidda mayaka ne, ɗari huɗu kuma masu harbi da kibau ne.
Sannan kuma ya faɗa cewar bai taɓa wuce wani gari a china ya dawo shiba face sai ya riski an taskance zanen fuskarsa a garin.
Acewarsa, mutanen kasar nayin haka ga kowanne bako saboda koda zaiyi laifi ya gudu, sai su aika da fuskarsa sassan duniya ta yadda da anganshi za'a kame shi.
Ibn Battuta ya kayatu da kyawun gine ginen garin Constantinopole na kasar egypt. Haka kuma ance ginin cocin Saint Sophia yayi matukar burgeshi, amma yaki yarda ya shiga cikinsa saboda ya lura idan ya shiga tilas ya russunawa gicciye na kiristoci.
Akwai kuma labarin daya bayar mai nuna gudun duniyarsa da rashinsa ga kwaɗayi, wanda yace wata rana suna tare da sarkin ceylon yana cin wasu zaɓaɓɓun Inibai, sai sarkin yake tambayarsa ko ya taɓa ganin inibai masu kyawun waɗannan?
Nan take Ibn Battuta yace tunda yake shige kasashe, bai taɓa ganin inibai kamar suba.
Wannan sai yasa sarkin yaji daÉ—i, har ma yacewa Ibn Battuta ya kwashe duk iniban ya bar masa su kyauta. Amma sai Ibn Battuta ya kalli abin a matsayin kaskanci, sannan yace da sarkin shifa ba wannan ne damuwar saba, abinda yafi bukata shine yaga sawun kafar Annabi Adamu da akace akwaishi a kasar.
Tabbas Ibn Battuta ya rayu cikin ilimi da imani.
Da fatan Allah yajikansa amin.
Post a Comment (0)