TAMBAYA:- Slm Dan Allah macen da batayin al'ada kuma anyi awon ciki babu cikin mecece matsalar ? Sannan Jinkirin Haila nada alaqa da rashin haihuwa ?
AMSA :-
✍️ DA FARKO MENE JINKIRIN HAILA (AMENORRHEA) ? :
Jinkirin haila shi ne samun tsaiko ko jinkirin al’ada tsawon wata biyu ko fiye da haka.
Sannan Jinkirin Haila Ya kasu kashi biyu : akwai
1- Primary Amenorrhea
2- Secondary Amenorrhea
♦ 1- primary Amenorrhea : shine jinkirin rashin yin hailar mace har takai shekaru goma sha shidda zuwa sama bata fara haila ba.
♦ 2- Secondary Amenorrhea : shine macen da dama Chan tana ganin hailarta normal sai yadaina zuwa mata.
✍️ MEYAKE KAWO JINKRIN HAILA??
abubuwa da dama suna kawo jinkirin Haila, ga kadan daga ciki :
1- Pregnancy.
Mafiyawan mata idan sun dauki ciki sun daina ganin hailarsu.
2- Lactating
Akoi mata da dama idan suna shayarwa basa ganin hailarsu.
3- Infection
Yana daga cikin abubuwanda yake kawo jinkirin Haila sun hada da shigar kwayoyin cuta a mahaifa, kamar ta hanyar kamuwa da ciwon sanyi.
4- Family Planning Pills
Shan wassu daga cikin kwayoyin hutun haihuwa (a cikinsu akwai masu rikita haila, akwai kuma wadanda suke saita Haila )
5- Family planning injection e.g Depo-provera.
Amfanin da allurar hutun haihuwa kamar su Depo Provera.
6- ovarian cyst
kumburin kwan mace da ake cewa ovarian cyst shima yana rikitar da Haila.
7- Stress
Rashin kwanciyar hankali kaga mace kullum ta tada hanakalinta akan wani Abu shima yana rikitar da Haila.
8- Regular Strenuous Exercise.
Motsa jiki mai tada hanakali kamar gudu zuwa waje mai Nisa.
9- Extremely Low Body Weight.
Rashin nauyin jiki wanda ake samu Sabida rashin isheshahen abinci lafiyayya.
10- Diseases
Wasu cututtuka kamar su zazzabin typhoid, ko tari.
11- Problem with thyroid
Masalar thyroid gland wanda yake kawo hormones.
12- Then certain types of medicine, such as antidepressants, chemotherapy etc.
✍️ SHIN JINKIRIN HAILA YANA DA ALAKA TA RASHIN HAIHUWA ??
Duk wadannan sukan iya kawo rashin haihuwa ko jinkirin samun juna biyu, domin shi samun juna biyu yana bukatar yanayin al’ada daidaitacce ba rikitacce ba .
MATSALAR ZUWAN AL-ADAH (Menstrual Disorder).
Mafi akasarin matasuna famada matsalar zuwan al-adah wadda wasu yakansa sushiga damuwa,bisa rashin sanin yazasu maganceta,,matsalolin sune kamar haka.
1_ DYSMENORRHEA (pain menstruation).
matsalace dake haddasa al-adah mace take zuwa da zafi, wadda Shima yakkasu Kashi biyu:
a-spasmodic dysmenorrhea:
shikuma yafi ta'allaqada zafinsa wajen Mara (uterine) Kuma sai lokacin al-adah yakefaruwa, kusan Rabin mata sunafamadashi, yawancinsa yakan farawa daga shekara 17yrs zuwa 28yrs.
Kuma Yadanganta da wata takan finwata,Yadanganta da jin,dakuma motsa tsokarwajen,wani lokacin har rashin zuciya yakesawada gudawa.
b-congestive dysmenorrhea:
shikuma wannan yafi faruwa ga manya, yakansa ciwon baya,ciwon qugu,dakuma yawan baccin rai nababu dalili, Mafi akasari zafin yakan daukar kwana biyu zuwa uku kafin al-adah.
2_AMENORRHEA/OLIGOMENORRHEA,(Absence of menstruation).
shikuma wannan matsalace dake dauke zuwan al-adah gabadaya.
ababen dasuke kawoshi sunhad'ada, PID, qari a fibroids , endometriosis, matsalar kwayaar halitta(chromosomal defect)Kamar tuner syndrome, asalina ahali,sadai sauransu
3_MENORRHEA (Yawaitar fitar jinin al-adah).
wannan shikuma yakan faru kodai yayi tsawo,kokuma yakezubada yawa, yakan haddasa qari a ovaries, da PID, dakuma grandier cell tumour, hormonal imbalance. up
4_EPIMENORRHEA (daurin juyowar al-adah),
Mafi akasarin mata sukanyi cycle dinsu awajen 26-28day, shikuma wannan yakan juyowa daga 14-21day, wannan yakan farune Mafi akasarin idan anyi abortion (zubarda ciki),kokuma haihuwa.
5_METRORHAGIA:
shikuma wannan matsalar tanasa zubar jini(bleeding) haka kawai karazube, Kakasa ganewa na al-adane ko akasin haka ,
yawanci wannan yakanfarune saboda cututtuka Kamar, trachomonas, vaginatitis, cervical erosion,incomplete abortion,PID dasauransu..........
GA HANYA MAFI SAUKI YADDA MACE ZA TA GANE OVULATION PERIOD NATA :
OVULATION shine wani lokaci da mace ke fafe kwan haihuwarta Wanda da zaran ta fafe ta kusanci miji to shikenan sai ciki da ikon Allah.
lokacin ovulation lalle idan kina da kula zaki gane. Yakamata mu dinga kula domin akwai wani irin painless contraction da zakiji.mun san fallopian tubes dinmu guda biyu hagu daya a dama daya. So duk wata daga gefe daya ne kwan zai fito
1- farko shine painless contraction zakiji wani irin ciwo a hagu ko dama.
2- zaki dinga jin menstrual pains slightly amma ba menses kikeyiba
3- Areola wato black point na nononki zai kara baki kuma nipple wato kan nononki zai mike yayi erect kuma akwai zafi kadan kadan musamman idan ana tabawa
4- Vaginal fluid. Majina mai tsananin danko Wanda take zama kaman spring zai dinga fito miki a gabanki
5- Matsananciyar Shaawar namiji kamar yadda muka bayya na a baya.
6- Rising na temperature, ma'ana zafin jiki.
Idan bakye gane ta alamu ga bayani dalla dalla yadda zaki kirga lokocin ovulation naki:
1- Idan mace jinin hailan ta yana zuwa a kwana 22 , to za tafara kirga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana takwas (8) , a kwana na takwasdin nan ana kyeutata zato itace ranar ovulation nata.
2- Idan mace jinin hailan ta yana zuwa a kwana 23 , to za tafara kirga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana tara (9) , kwana na taran (9) ana kyeutata zato itace ranar ovulation nata.
3- Idan mace jinin hailan ta yana zuwa a kwana 24 , to za tafara kirga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana Goma (10) , kwana na goman (10) ana kyeutata zaton itace ranar ovulation nata.
4- Idan mace jinin hailan ta yana zuwa a kwana 25 , to za tafara kirga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana (11) , kwana na Shadayan (11) ana kyeutata zaton itace ranar ovulation nata.
5- Idan mace jinin hailan ta yana zuwa a kwana 26 , to za tafara kirga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana (12) , kwana na Shabiyun (12) ana kyeutata zaton itace ranar ovulation nata.
6- Idan mace jinin hailan ta yana zuwa a kwana 26l7 , to za tafara kirga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana (13) , kwana na Sha'ukun(13) ana kyeutata zaton itace ranar ovulation nata.
7- Idan mace jinin hailan ta yana zuwa a kwana 28 , to za tafara kirga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana (14) , kwana na Sha'hudun (14) ana kyeutata zaton itace ranar ovulation nata.
8- Idan mace jinin hailan ta yana zuwa a kwana 29 , to za tafara kirga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana (15) , kwana na Shabiyar (15) ana kyeutata zaton itace ranar ovulation nata.
9- Idan mace jinin hailan ta yana zuwa a kwana 30 , to za tafara kirga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana (16) , kwana na Sha'shidda (16) ana kyeutata zaton itace ranar ovulation nata.
10- Idan mace jinin hailan ta yana zuwa a kwana 31 , to za tafara kirga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana (17) , kwana na Shabakwan (17) ana kyeutata zaton itace ranar ovulation nata.
11- Idan mace jinin hailan ta yana zuwa a kwana 32 , to za tafara kirga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana (18) , kwana na Sha'takwas din (18) ana kyeutata zaton itace ranar ovulation nata.
12- Idan mace jinin hailan ta yana zuwa a kwana 33 , to za tafara kirga daga ranan da taga jinin hailanta zuwa kwana (19) , kwana na Sha'taran (19) ana kyeutata zaton itace ranar ovulation nata.
MEYASA MATA KE GANIN FARIN RUWA YANA FITO MUSU KAFIN KO BAYAN GANIN PERIOD
DIN SU?
AKWAI MATSALA NE TATTARE DA HAKAN?
✓Normally mafi yawan mata suna samun fitowar farin ruwa a gabansu throughout menstrual circle dinsu.
✓Akalla mata dayawa suna ganin farin ruwa mai kauri ko salala, mara launi yana fito musu a kowace rana, adadin daya kai kimanin cikin shokalin shayi. Launin ruwan yana iya sauyawa daga farin madara, zuwa farin ruwa, ko kuma baki baki (brown).
✓Banbancin launin ruwan ko kaurin sa yana ta allaqa ne da hormonal changes na jikin ta a lokacin da yake fitowa.
✓Wannan fitan farin ruwa da mace take gani ta gaban ta kafin period dinta normal ne, babu matsala tattare da hakan. Process ne da ake kira "Leukorrhea" Wani lokacin yana iya kasance wa yellowish.
✓Hakan yana faruwa ne sbd yawan hormones "progesterone" dayake taruwa ajikin ta. A wannan gaban ana kiran yanayin da "luteal phase"
✓Wa'ennan hormones kamar su"progesterone" "oestrogen" "androgen" etc sauyin yanayin sune ajikin ta shike sawa tayi ta ganin "vaginal discharge" yana fito mata.
✓ Idan "estrogen" ne sukayi yawa ajikin ta a lokacin, se ruwan ya kasance fari fari, mai yauki
kuma ruwa ruwa.
✓ Idan kuma "progesterone" ne sukayi yawa ajikin ta, se ruwan ya kasance farin madara kuma mai kauri kauri.
✓Koma ya launin ruwan ya kasance, fari ne, ruwa ruwa ne, madara madara ne, yana da kauri ko akasin haka, muddin baya wari ko qarni, gaban mace baya zafi, kaikayi ko radadi, to wannan normal ne.
✓Aikin sa (ruwan) shine yayi flushing duk wani dattin vagina, wasu harmful germs, etc da kuma ya sa vagina ta zama moist all the time. Hakan yana nuna alamar the vagina and the
reproductive system is healthy and functional.
• WASU LOKUTA NE ZAKI TSAMMANCI GANIN FARIN RUWA A GABANKI; IDAN KINGANI BA DAMUWA BANE.
✓Normally mata suna iya samun bushewar gaba kamar na kwana 3 zuwa 4 kowane bayan yankewar period dinsu. bayan wannan kwanakin, farin ruwa mai danqo yakan sake bullowa wanda zayyi kamar kwana 4 zuwa 5 Kafin ovulation, alama she ta eggs sun fara developing. ana kiran shi da "follicular phase" that means a lokacin ne "eggs" (for ovulation) suke kokarin girma.
✓Idan kuma lokacin ovulation yayi, ruwan se ya
canza daga mai danqo zuwa fari mai yauki kuma mara kauri (salala) haka. A wannan lokacin yana kara yawa sosai fiye da na kullum a da. Shi kuma ana kiran shi "egg white".
Aikin sa shine ya taimaka wajen santsin sperm a vagina da cervix domin ya samu daman isowa kwai da yake jiransa for ovulation.
✓Sannan Mata dayawa suna amfani da ganin wannan ruwan a matsayin alama ta ovulation dinsu, hakan yana taimaka musu wajen samun ciki da wuri ko kuma kaura cewa yin cikin. Wannan process din shi ake kira da "natural family planning" ko "fertility awareness method".
1. ✓Idan ruwa ruwan ya kasance mara kauri (salala) to ana kyautata zaton shine "fertile" (i.e ciki zai iya shiga kenan in Kwan ya samu sperm). Sbd a lokacin kwan zai sauka zaman jira.
2. ✓ Idan kuma ruwa ruwan ya kasance fari mai kauri to shi kuma shine "infertile" (wanda ko an sadu ciki bazai shiga ba) sbd kwan har ya riqa, karfin sa ya kare, yanzu sedai ya harziqa, se facewa.
✓To irin wannan ruwa ruwan mai kauri zaki cigaba da gani daga bayan ovulation har zuwa wani period din.
✓Daga bayan ovulation din zuwa wani period din, yawan fitowar ruwan zai na raguwa a hankali, yana zamowa mai kauri kuma mai danqo again, wani lokaci har zaki iya jinsa kamar wata gum ko glue.
✓On average dai, yana kaiwa irin kwana 11 zuwa 14. That is tsakanin ovulation dinki zuwa wani period dinki kenan.
✓Wasu lokuta kina iya ganinsa yellowish haka kafin period dinkin.
✓Idan mace taga wani irin brown discharge a bayan period dinta kuma, bayan jinin ya dauke, se ta sake ganin wani baki baki haka brown ya zo mata, to shi din yana kasance wa tsohuwar jini ne daya daskare bai samu daman fitowa ba last time. Shine yanzu yake kamo hanya.
✓Idan kuma brown discharge din kafin period ne fa? Ko kuma taga jinin Dan digo digo haka a lokacin da take tsammanin period dinta, to shi
kuma yana iya kasance wa sign ne na "implantation" daga farko farkon pregnancy. Maza se kiyi kokari kije pregnancy test domin a tabbatar da hakan ko akasin hakan. (In kin samu congratulations )
• ME KE JAWO KO SANADIN FITOWAR FARIN RUWAN?
Akwai kamar category guda biyu:
1. Akwai wanda yake normal; sbd hormonal
changes.
2. Akwai kuma wanda yake abnormal: sbd infection.
1. NORMAL:
(A1).✓ yana iya kasance wa alama she ta reproductive system na mace yana functioning properly. Sbd kasance war discharge din mara kauri ne, mai yauki ne kuma mai santsi. Sannan baya wari ko qarni. Wasu suna kiran shi da "egg white mucus"
(B1). ✓Normal side effects na family planning; sakamon sauyin yanayin levels na hormones da yake jawowa, hakan yana sawa normal vaginal discharge ya karu shima.
(C1). ✓Pregnancy: wani lokaci yawan vaginal discharge kafin lokacin normal period dinki yazo yana iya zama sign ne na daukan ciki. Musamman ma idan mucus din ya kasance mai kauri kuma ruwan madara madara.
2. ABNORMAL:
(A2). ✓STIs(Sexually Transmitted Infections): kamar su Gonorhea, chylamydia, Trichomonas duk suna jawo mace tayi ta ganin fitan ruwa ta gaban ta. Gonorhea da chylamydia su yawanci basa ma nuna symptoms, sannan discharge dinsu yana nan ne yellowish haka kamar diwa diwa.
✓Shi kuma Trichomonas; discharge din da yake jawowa yana yellow ko Kore ne haka, sannan yana nuna symptoms dinsa kamar qarnin kifi kifi, kuma ga kaikayin tsiya.
(B2). ✓Candidiasis (yeast infection): shi kuma discharge dinsa fari ne mai kauri, kamar farin madara. Yawanci yafi faruwa a lokaci kafin mace taga period dinta. Yana da symptoms kamar kaikayi da jin zafi zafi a gaban mace (ta ciki da ta wajen).
(C2). ✓Bacterial Vaginosis: shima wata infection dinne da yake jawo discharge mai Kama da toka toka(gray-white) sannan yana sa warin gaba kamar qarnin kifi kifi haka.
✓ Kamar yadda kuka gani a sama tin farko, ainihin ababen da ke sa fitowar farin ruwa kenan. Da kuma yawancin lokuta da ruwa yake fito ma mata.
SHAWARA
✓Duk sanda kika ga ruwa yana fitowa ta gaban ki, kana fari ne, milk milk ne, mai kauri ne ko salala ne, mai yauki ne ko mai santsi ne, muddin baya wari kuma baya sa kaikayi ko radadi ko jin zafin gaba ko kuma yayin fitsari ko saduwa da miji, kawai ahlun salun yake fitowa abinsa, to karki tada hankali wannan normal ne. Alama she na jikin ki a matsayin ki mace, yana aiki yadda yakamata kuma cikin kocin lfyy.
✓Idan kuma kinga ruwa yana fito miki koma ya launin sa yake, kuma se tare da hakan akwai zafin gaba, kaikayin gaba, ko warin gaba, kumburin gaba, kurajen gaba ko dadewar fatar shi, ta ciki ko ta wajensa, ko kuma duka biyun, to maza maza kiyi saurin zuwa asibiti domin magani.
Allah Yabamu Lafiya Gabaki Dayanmu.