MENENE HUKUNCIN MAI ZUWA GIDAN ABOKIN SA, ALHALI BAYA NAN?

MINENE HUKUNCIN MAI ZUWA GIDAN ABOKINSA, ALHALI BAYA NAN?

                               Tambaya:

Malan menene hukuncin mai zuwa gidan abokinsa yana fira da matarsa alhalin abokin nasa bayanan?
(Daga Abdullahi Baban Saifalah).


                                  Amsa

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
A'a wannan bai halatta ba, yin hakan kusancine ga aikata zina.‎ Saboda hadisin Manzon Allah (S.A.W) wanda yake cewa: "LAA YAKLUWANNA AHDUKUM BI IMRA'ATIN ILLA MA'A ZY MAHRUMIN"

                                 Fassara

"Kada dayanku ya kadaita da wata mace sai tareda  maharruminta.

                                  Ma'ana

Dan uwanta wanda babu aure a tsakaninsu, kamar wanda suke uwa daya ko uba daya ko kuma uwa daya uba daya ko makamancin haka.

A Wani hadisin kuma yana cewa:
" ﻻ ﻳﺨﻠﻮﻥ ﺭﺟﻞ ﺑﺎﻣﺮﺃﺓ ﺍﻵﻛﺎﻥ ﺛﺎﻟﺜﻬﻤﺎﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ "

Abinda hadisin yake koyar damu shine: "Duk wanda ya kadaita ma'ana ya ke6anta da‎ wata mace wacce ba muharramar saba, to zai kasance na ukunsu shaidanne. To kaga kuwa wata rana idan sha'awarta ta motsa komai zai iya faruwa kasancewar babu mai dauke mata sha'awar tata a kusa.

Saboda haka bai halattaba, aikata hakan zunubine mafi girma.

WALLAHU A'ALAM

Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)