*"TUN YAUSHE NE RABONKA DASHI".......?*
_"Jama'a *Al'qur'anin* nan fa shine dukkanin tushen addinin mu, acikinsa ne muka fahimci mecece manufar addinin mu na musulunci, to wane dalili ne zaisa mu ƙaurace masa bayan shi kuma shiriya ne a gare mu, shi ceto ne a garemu"?_
*_"Mutane da yawa acikin mu sun manta rabon da su ɗauki alƙur'ani mai girma su karanta shi, wasu tunda watan Ramadana ya wuce basu sake buɗe shi ba domin su karanta shi, wasu kuma sun ɗan buɗe shi na ɗan lokaci kaɗan bayan wucewar Ramadana ɗin, wasu kuma sun rabu dashi har yayi ƙura akansa sabida ba'a taɓa shi, to kai yaushe ne rabonka dashi"?_*
"Koda yake! ai daman wasu kam ko zuwan Ramadan ɗin baisa sun mayar da alƙur'ani mai tsarki abin karantarwar su ba, sun ƙaurace masa haƙiƙanin ƙauracewa"
*_"Kai wasu ma sai su kwashe shekara guda ba tareda sun karanta shi ba, wannan kuma itace babbar asara ga rayuwar ɗa musulmi"_*
_"Yããã Allah Kasa Muzama Cikin Masu Karanta Al'qur'ani Akoda Yau She"_
✍🏽 *_Y Adam Maiha_*
Telegram: https://t.me/YusufAdamMaiha