Fassarar Kalaman Fim Din Ek Villain
Shekarar Fitw- 2014
1
Jab tak hum kisi ke humdard nahi bante ... tab tak hum dard se aur dard humse juda nahi hota
Matukar Wani bai tausaya mana ba... Idan har hakan bai faru ba to ba zamu rabu da bakin ciki ba kuma shima ba zai rabu da mu ba
Shraddha Kapoor
2
Nafrat ko nafrat nahi, sirf pyar mitta sakta hai ... bas zaroorat hai kisi ke haath ki ... joh kheench kar usse andheron mein se ujalon mein la sake
Kiyayya bata goge Kiyayya, So ne kawai ke yin hakan... Hannu kawai kake bukata... Wanda zai tsamo ka daga Duhu izuwa haske
Shraddha Kapoor
3
Zindagi ko aaisi party ki tarah jeena chahti hoon ki maut jab aaye na ... toh saath behetkar do drink maarkar, jaan lekar chali jaye
Ina so in rayu ne tamkar ina wurin Shagali saboda duk lokacin da mutuwa tazo... Zata dan sha abinsha ko biyu ne tare dani kafin ta dauke ni.
Shraddha Kapoor
4
Main tujhe marne nahi doonga ... lekin main tujhe roz maaroonga ... ek baar nahi hazar baar maaroonga
Ba zan Barka ka mutu ba... Amma Zan kashe ka kullum... Ba sau daya ba, zan kashe ka ne Sau Dubu
Sidharth Malhotra
5
Muskurane mein na koi tax nahi lagta
Babu wani Haraji (da za'a caje ka) yayinda kayi murmushi
Shraddha Kapoor
6
Zindagi mein ek hassi woh hoti hai joh insaan apne gham ko chupane ke liye khud seekhta hai ... aur ek hassi woh hoti hai joh insaan ke saare gham bhula deti hai
A rayuwa akwai wani irin murmushi guda daya wanda mutum yake koya da kanshi domin ya boye damuwar sa.. Sannan kuma akwai wani irin Murmushi guda daya da ka iya sa mutum ya manta da duk wata damuwar sa.
Asif Basra
7
Andhere ko andhera nahi ... sirf roshni mitta sakti hai
Duhu baya kawar da Duhu... Haske ne kawai ke yin hakan
Shraddha Kapoor
8
Tere jism se behte khoon ke har ek katre ka hisaab rakhoonga main ... teri aakhri saans ko bhi mutthi mein bandh rakhoonga main ... tujhe itna maroonga ki dard jeete ji tere jism ko bhi hoga ... aur cheenk marne ke baad tere rooh se bhi niklegi
Zan Kiyasce kowane digon jinin ka da zai zuba daga jikin ka... Zan boye Numfashin ka na karshe a cikin tafin hannu na.... Zan dake ka iya duka ta yadda jikin ka zai ji zafin yayinda kake raye... Kuma ruhinka zai dinga ihu ko bayan mutuwar ka.
Siddharth Malhotra
9
Kehte hain maut bin bulaye aa jaati hai ... lekin main maut ke samne roz khada ho jaata hoon ... begani shaadi mein Abdullah deewana bankar
Akan ce Mutuwa takan zo ba tare da katin gayyata ba... Amma ni ina tsaye ne a gaban mutuwa kullum... Tamkar dai bakon da yaje bikin da ba'a gayyace shi ba.
Sidharth Malhotra
10
Tum sabki nikalti jaan ke saath ... meri har chinta, sari stress bhi nikal jaati hai
Yayinda Rayukanku ke Rabuwa daku... Duk damuwa ita ma takan tafi a binta
Ritesh Deshmukh
11
Main jaanti hoon tum doli sajake rakhne waalon mein se nahi ho ... goli chalake thokne waalon mein se ho
Nasan cewa kai ba irin mutumin da zai zo da kayan wasa bane... A Maimakon hakan kai mutum ne wanda zai iya harba bindiga kuma yayi kisa
Shraddha Kapoor
12
Jab tera dard kam ho jayega ... jab tera har zakhm bhar jayega ... main phir aaonga tujhe naye zakhm dene ... aaj se yahi hai tera muqaddar, yahi hai teri sazaa
A Duk Lokacin da zafin jikin ka ya ragu... Sa'ilinda Ciwukanka zasu warke... Zan sake dawowa in baka wasu sabbin Ciwukan... Daga yau wannan Itace Kaddarar ka kuma Hukuncin ka
Sidharth Malhotra
13
Shaitan ki ek khasiyat hai ... apne hi janaze mein shamil hona uski fitrat hai ... nafrat uska hathyar, gussa uska barood ... humdardi usse aati nahi aur pyar koi usse karta nahi
SHEDAN ya kware akan abu guda daya... Abu ne Sananne dangane da shi cewa yana zuwa wajen Jana'izar sa... Kiyayya ce Makamin sa, Fushi shi ne Tokar bindigar sa... Bai san tausayi ba kuma bashi da Masoyi
14
Gunahgar hamesha wahi lautta hai jahan usne gunah kiya hai ... aur aashiq hamesha wahi lautta hai jahan usne aashiqui ki hai
Dan Ta'adda a koyaushe yakan koma inda ya aikata ta'addanci... Shi kuma Masoyi yana komawa inda yayi soyayya
15
Har love story mein ek hero hota hai, ek heroine aur ek villain
a kowane labarin soyayya akwai Jarumi, akwai Jaruma Da Kuma Azzalumi
16
Zyadatar insaan pehda hota aam hai, jeeta aam hai, marta aam hai ... bade parde pe ya duniya mein na sahi ... kam se kam usse apne ghar pe, apne apno ke nazaron mein toh hero hona chahiye
Sau da yawa akan haifi mutum ne a matsayin talaka, ya rayu a talaka, ya kuma mutu a talaka... Watakila a Fim ne ko kuma a fili... Amma dai a kalla ya kamata ace ya zama Jarumi a cikin gidansa, a gaban masoyan sa
Ritesh Deshmukh
17
Tu jitna marne ke liye marega ... utni hi tujhe zindagi milegi
Iya kokarin ka na ka mutu... Iya tsawon rayuwar da zaka samu.
Sidharth Malhotra
18
Is andhere ko roshni koi diya nahi ... sirf teri chitta ki aag de sakti hai
Babu wata Fitila da zata iya baiwa wannan Duhun... Sai dai wutar Konewar ka.
Sidharth Malhotra
19
Aaj ke baad aapko shikayat ka mauka nahi milega
Daga yau ba zaki sake damar yin Korafi ba
Ritesh Deshmukh
20
Tum sabke dard mein mujhe khushi nahi milti ... sukoon milta hai
Tare da bacin ranku duka ba wai farinciki kawai nake samu ba... Ina samun nutsuwa
Ritesh Deshmukh
21
Hum middle class log hai ... upper class aur lower class ke beech mein sandwich bane huye hai
Mu fa Matsakaitan mutane ne... Wadanda suke tamkar dambu a tsakanin Masu kudi da Talakawa
Kamaal Rashid Khan
@HaimanRaees
08185819176
Haimanraees@gmail.com