HUKUNCIN KYAUTAR LADAN IBADA GA ANNABI S.A.W...?
Tambaya
Assslam alaika warahamatullah wabrakatuhu malam ina maka fatan alkairi tambaya ta itace wani bawan Allah ne idan yayi sallah nafiloli sai yace Allah ya bawa Annabi ladan menene hukuncin hakan ya halatta ?
Amsa
To dan uwa wannan bidi'a ne ba addini bane kuma ya aikata abinda magabata basu yiba ya kamata mutum musulmi yasan abinda yake ya dinga aikata abinda shari'a tace yayi, wannan karancin tunani ne rashin sanin ya kamata ne ai kai baka isa kabawa Annabi S.A.W lada ba duk dunia babu wanda yakai Annabi tarin lada mai yawa kana tsammanin ladanka zai kara masa wani abu babu abinda zai kara masa domin Allah ya yafe masa idanma yayi kuskure don haka wannan bidi'ane ba addini bane kuskure ne a kiyaye abinda babu asali a musulunci.
Sannan ba'a daukan lada a bawa wani bazaka iya daukan lada kace na bawa wane ba kamar kayiwa iyayenka sallah ko karatun Alkur'ani kace a basu ladan sai dai kayi wani abu na sadakatul jariyya wadda zata riskesu
Allah shine mafi sani
Amsawa:- Dr. Abdallah Gadon kaya
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.