ZAN IYA HULDA DA MAI KUDIN LUKUDI?

ZAN IYA HULDA DA MAI KUDIN LUKUDI ?

                             Tambaya
Assalama alaikum. Malam dan Allah 

Ina aiki ne akarkashin wani Alhaji Amman a nazargin sa da wai kudinsa bana halal bane wasu suce dan luwadi ne wasu kuma suce kudin lukudu ne, ina so in san ya dace na cigaba da mai aiki ko inbari Allah ya kara lpy da ilimi da kaifin basira ameen

                               Amsa
Wa'alaikum assalam, Ya wajaba ka tabbatar da hakan kafin ka yanke hukunci.
Ba'a gina hukunci a musulunci akan shakka ko zato mara rinjaye, saboda wani sashen zaton zunubi ne kamar yadda aya ta (12) a cikin suratul Hujraat ta tabbatar da hakan.

Idan wani bangare na kasuwacinsa halal ne wani kuma Haram ne za ka iya hulda da shi, saboda Annabi S.A.W ya yi mu'amala da yahudawa kuma a cikin dukiyarsu akwai halal akwai kuma haram.

Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa

16/09/2017

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)