LADAR KOWANE TAKU ZUWA SALLAR JUMA'A

LADAR KOWANE TAKU ZUWA SALLAR JUMA'A

Kowane taku zuwa Sallar juma'a Ladar aikin Shekara na azumi da tsayuwar dare

Daga Ausi bn Ausi Assaqfy R.A yana cewa:-
"Naji Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
(Dukkan wanda yayi wanka a ranar juma'a wankan juma'a,Yayi sammankon zuwa da wuri sallar juma'a,ya tafi a kasa bai hau abin hawa ba,ya matsa kusa da Liman ya saurari khuduba,bai yi magana ba,yana da Ladar ko wane taku da yayi zuwa sallar juma'a,ladar azumin shekara da tsayuwar daren shekara).
@رواه أحمد وأبو داود والترمذي وصححه العلامة الالباني.

Malamai suna cewa;-
"Babu san wani hadisi da yafi wannan Hadisi dauke da lada da falala mai yawa ba kamarsa".

Ko wane taku yana daidai da ladar azumin shekara guda da tsayuwar dare da ibada na shekara guda,taku daya yana daidai da azumin kwana 365 da ibadar daren kwana 365.

Yana daga falalar Allah akan bayinsa ya sanyawa aiki dan kadan da lada mai yawa,wannan lada bata samuwa sai ga wanda ya cika sharudda guda biyar kamar yanda hadisi ya tabbatar.

SHARUDDAN SUNE
1-Yin wankan juma'a

2-Tafiya zuwa masallacin juma'a da wuri.

3-Tafiya Masallacin a kasa ba akan abin hawa ba

4-Halartar Khuduba

5-Yin shiru dan sauraran Khuduba*

  Allah ne mafi sani

Dan jin karin bayani game da wannan hadisi zaka iya sauraran babban malami daga cikin manyan malaman duniya a yanzu wato;-
👇👇👇👇👇👇👇👇
🎥 أسمع الشيخ صالح الفوزان 
     ماذا يقول عن هذا الحديث
https://m.youtube.com/watch?v=f0XEkO-bWEQ

Post a Comment (0)