Yadda Ake Fidda Zakka

YADDA AKE FIDDA ZAKKA

101. TAMBAYA:

yaya ake fidda zakkar amfanin gona?

AMSA:

watau in dai yakai NISABI, watau sa’I dari uku (300), shine Ausiki biyar (5), ko abinda ya wuce haka, sai a kasa shi kashi goma, ya bada kashi daya. Amma sai in ba wanda ake banruwa ba ne. amma in wanda ake banruwa ne, sai a kasa kashi ishirin ya bada kashi daya (wato noman rani).
.
Duk wadannan hukunci kuma, sai in ya zan ga kwaya (hatsi); wadanda ana iya ci kuma ana iya ajiye su, ba tareda sun lalace ba. Ban da kayan Lambu, ko dai wadanda ba’a iya ajiye su, kamar Doya, Rogo, ko Dankali ko kuma su Auduga, wadanda su ba abinci bane, su dukkan irin wadannan ba’a fidda musu da zakka, ko da kuwa mutum yayi su da yawa, ya sami kudinsu; duk da haka ba’a fidda musu da zakka, sai dai in kudin (Amfanin gonar) sun shekara; wannan kuma ya zan zakkar kudi (na amfanin Gona), bana ainihin noma ba. Saboda haka in kudin sun shekara sai ya raba su arba’in (40) ya bayar da kasha daya.
.
Wannan fatawa ne na Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi, na Musa Lawal Funtuwa wanda ni Abu Abdirrahman Kaltungo ke Gabatarwa.
.
Allah tabbatar da Malam a cikin aminci har ranar tashin qiyama.

1 Comments

Post a Comment