HUKUNCIN YIN DILKA

*_HUKUNCIN YIN DILKA_*

                            *Tambaya*
Mace ta ba da jikinta ga mata 'yan uwanta don a yi mata wanka saboda kwalliya ko irin dilka da halawa din nan wai haramun ne? Ko da ta rufe mamanta da mazaunanta? In haramun ne kenan daga ina zuwa ina ne tsiraicin mace da bai kamata 'yar uwarta mace ta gani ba? Jazakallahu khairaljazaaa.

                                *Amsa*
To 'yar'uwa malamai sun yi sabani game da tsaraicin mace ga 'yar uwarta Musulma, akwai wadanda suka tafi akan cewa : bai halatta 'yar uwarta mace ta ga wani abu a jikinta ba, sai abin da ya saba bayyana a tsakanin mata, idan suna zaune isu-isu, kamar kafa da hannu da fuska da wuya da makamacin haka.

Sai dai abin da mafi yawan malaman fiqhu suka tafi akai shi ne: al'aurar mace ga 'yar'uwarta musulma tana farawa ne daga cibiya zuwa gwiwa, kamar yadda al'aurar maza take a tsakaninsu.

Don haka bai hallata ta bari wata mace ta kalli sama da wannan wurin da aka iyakance ba, amma idan kafira ce matar to malamai sun yi bayani cewa ba za ta kalli wani abu ba, sai abin da ya saba bayyana, don haka sai a kula lokacin da za a je dilka wajen wacce ba musulma ba, don kada garin neman gira a rasa ido.
Sannan a bisa wannan bayanin da kika yi, dilkar da kika siffanta za ta zama ba ta halatta ba, tun da za a ga abin da shari'a ba ta hallatata a gani ba.

Allah ne mafi sani

Amsawa: Dr. Jamilu zarewa.
Gabatarwa: Abdullahi Gambo.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.

Post a Comment (0)