*_HUKUNCIN YIN KIRAN SALLAH BA TARE DA TSARKI BA!!!_*
*Tambaya*
Assalamu Alaikum, malam ko ya halatta mutumin da yake da janaba ya kira sallah ??
*Amsa*
To dan'uwa wasu daga cikin malamai suna cewa tsarki ba sharadi ba ne yayin kiran sallah, saboda babu wani nassi ingantacce wanda ya nuna hakan, don haka ya halatta ga mai janaba, da mai karamin kari su yi kiran sallah, saidai abin da ya fi shi ne yin cikakken tsarki kafin kiran sallah, saboda fadin Annabi ﷺ "Ina kin na ambaci Allah alhali ba ni da tsarki", kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 16, kuma Albani ya inganta shi a Sahihu-sunani Abi-dawud 1\16.
Don neman Karin bayani duba: Fathul-bary 3\113 da Majmu'u fataawaa wa makaalatin mutanawwi'a 10\338.
27/1/2015
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.