TAMBAYA
========
👇
Asslamu alaikum malam barka da safia an tashi lafia ya yaran. Malam kasancewar ance yin addu'a a sujjada tana karbuwa to mutum zai iyayin addu'ar koda a sallah farillah ne ko sai a nafila akwai aka yadda nayi addu'a cikin sujjadah?
AMSA
=====
👇
Zaka iya yi a kowacce sallah, farillah ko ta nafila, amma dai da zakayi a nafila zaifi, Sabida a sallar nafila kai kadai ne.
Kuskuren da wasu sukeyi, sai liman ya dago daga sujuda amma Su bazasu dago ba Sabida wai suna yin Addu'ah, wanna gaskiya babban kuskure ne, Malamai suna magana akan hakan, idan har kana son dadewa kana yin Addu'ah ne, to a sallar dare zaifi.
Saboda an samu magabata suna yi ne musamman ma a sallar nafila.
Akwai wani tabi'i da ake cewa UWAISUL KARNI, yana yin sujuda tin bayan sallar isha'i, idan ya ajiye goshinsa baya dagowa sai yaji ance ASSALATU KAIRUN MINANNAUM.
Kaga kenan idan da dare ne kana da damar da zakayi sujuda har sai ka gaji, kuma ba wanda yake ganinka, gashi kuma shi kansa lokacin karbar Addu'ah ne.
Amma ba a sallar la'asar ko azuhur ko magriba ba kana sallah liman ya dago kai baka dago ba.
Allah shine masani.
✍
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876