ZAKKAR GIDAN HAYA DA MOTAR HAYA

*_ZAKKAR GIDAN HAYA DA MOTAR HAYA_*

                             *Tambaya*
Assalamu alaikum Malam Shin ko akwai zakka akan Gona, Fili ,Gidan haya da Motar Haya?

                                  *Amsa*
Waalaikumussalam, To dan'uwa duk gonar da aka rika don ayi amfani da ita, to babu zakka a cikinta, haka nan fili, amma idan kasuwanci ake yi da su, kamar a siya a sayar to za'a fitar musu da zakka, idan sun cika nisabi kuma shekara ta zagayo musu, ko kuma ya zama  sun cika sharudan zakka idan ya hada su da abin da ke hannunsa.

Haka nan babu zakka a cikin gidan haya saidai idan aka tara kudin kuma shekara ta zagayo akan su, sun cika nisabi, to anan ne za'a fitar musu da zakka, ko kuma ya zama sun cika sharudan zakka idan ya hada su da abin da ke hannunsa.

Allah ne ma fi sani.

18/12/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)