ZAN IYA YAYE YARONA BA TARE DA SANIN MAHAIFINSA BA?

44. ZAN IYA YAYE YARONA BA TARE DA SANIN MAHAIFINSA BA?


*_Tambaya:_*
Assalamu Alaikum. Tambaya nake da shi kan yaye, zan iya yaye yaron da ya fara cin abinci ba tare da sanin mahaifinsa ba?

*_Amsa:_*
Wa Alaikum Assalam. Cimma daidaito game da lokacin yaye yaro kafin ya cika shekaru biyu tsakanin uwa da uba shi ne abin da yake daidai, kamar yadda aya ta 233 a Suratul Baƙara ta yi bayani. Idan uwa ta yaye yaro ba tare da izinin mai gidanta ba, za'a iya samun saɓani da fitintinu, tabbas shawartar juna yana kaiwa zuwa ga ra'ayi makatarci da kuma kaucewa kuskure.
_Allah ne mafi sani._

*_Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa_*

3 Comments

Post a Comment