CIMMA MASLAHA LOKACIN RABON GADO ABU NE MAI KYAU

*CIMMA MASLAHA LOKACIN RABON GADO, ABU NE MAI KYAU!!*

*Tambaya*

Assalamu Alaikum , malam Don Allah ya rabon gadon Wanda ya mutu yabar mata uku tsawon shekara bakwai kenan, suna zaune a gidan da ya barsu dashi, kowa a cikinsu tana da daki ciki da falo, bayi daya suke amfani dashi da tsakar gida. ta farko tana da namiji guda daya  da mata biyar, ta biyu tana da maxa hudu da mata shida, ta uku tana da namiji daya da mata hudu . don Allah mal ya gadon xai kasance, Allah yasaka da alkairi ameen

*Amsa*

Wa alaikum assalam
Abin da ya fi shi ne ayi Masalaha wani ya sayi gidan a cikin Magada sai a raba gadon kudin a tsarin da aka raba dukiyar mamacin a farko.

Akwai yiwuwar samun rikici nan-gaba Idan aka yi rabon gadon gidan Kamar yadda waccan matar take so, saboda 'ya'yan mutumin da matansa sun haura (20), Dakunan gidan kuma ba su kai (10) ba Kamar yadda kika bayyana.

Idan kuma  wani a cikinku zai yi Balantiya ya sayi gidan ya bar shi WAKAFI gare ku, ta yadda Kowa a cikinku zai amfana da shi, babu wanda zai ji na shi ne to hakan ne ya fi, saboda Za'a kiyaye zumunci kuma za ku dinga tunawa da gidan da mahaifinku ya Rayu a ciki.

Allah ne mafi sani

*Dr Jamilu Zarewa*

22/04 /2016

Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

Post a Comment (0)