AL-QUNUT A SALLAH:



AL-QUNUT A SALLAH:

TELEGRAM👇🏻
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

*TAMBAYA*❓

As-Salaam Alaikum.
A kan Al-Qunut a sallah shin a sallar farilla ce ake yi ko kuwa a nafila? Kuma kafin karatun Fatiha ne ko kuwa kafin Ruku’a?


*AMSA*👇

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Abin da ake nufi da Al-Qunuut a nan shi ne: Tsawaita tsayuwa a cikin wani sashe na Sallah domin yin waɗansu addu’o’i, bisa yadda ingantattu hadisai suka nuna.
Malamai sun yi magana a nan, a kan nau’i uku ne kawai:
(i) Al-Qunuut a cikin Sallar Witri.
(ii) Al-Qunuut a lokacin aukuwar wata masifa.
(iii) Al-Qunuut a cikin Sallar Asubah.
Bayani a kan waɗannan shi ne kamar haka:

 *(i) AL-QUNUUT A WITRI* 
Wannan nau’in shi ne wanda ya zo a cikin hadisin Al-Hasan Bn Aliy (Radiyal Laahu Anhumaa) cewa:
Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya karantar da ni waɗannan kalmomi, domin in riƙa faɗin su a cikin Sallar Witri:
Sai ya karanto Addu’ar Al-Qunut ɗin.
Al-Ameer As-San’aaniy ya ce: ‘Wannan hadisi dalili ne a kan cewa, Al-Ƙunuut a sallar Witri shari’a ce.’ (Subulus Salaam: 1/186).
Imaam An-Nawawiy ya ce: ‘Wannan hujja ce ƙwaƙƙwara ta fuskar dalili.’
Fiqhus Sunnah: 1/233.
Wannan nau’in na Al-Qunuut ana yin sa ne bayan an ƙare karatu a raka’ar ƙarshe na witri, kafin a yi ruku’u. Haka Ahmad, da Abu-Daawud, da An-Nasaa’iy, da At-Tabaraaniy da Al-Baihaqiy suka riwaito da isnadi sahihi. (In ji Shaikh Albaaniy a cikin Sifatus Salaah: 160).

 *(ii) AL-QUNUUT A LOKACIN MASIFA* 
Idan wani bala’i ya sauka a cikin al’ummar musulmi kamar yaƙi, ko fari, ko dai wata annoba makamanciyar haka, shari’a ta yarda a yi Al-Qunuut a cikin sallah, domin neman Allaah Maɗaukakin Sarki ya yaye wannan bala’in, kuma ya kawar da shi kwata-kwata. Wannan shi ake kira: Qunuutun-Naazilah ko Qunuutun-Nawaazil.
Asalinsa Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ne ya aika da waɗansu mahardata, masana Alƙur’ani guda saba’in daga cikin Sahabbansa zuwa wurin waɗansu ƙabilun Larabawa, domin su kira su zuwa ga musulunci. Amma sai waɗansu mutane suka tsare su a kan hanya, kuma suka kashe su gaba ɗaya! Shi ne Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi wa Alihi wa Sallam) ya ɗauki tsawon wata guda yana yin Al-Qunuut a cikin dukkan sallolin Farilla guda biyar: Azahar, da La’asar, da Magrib, da Ishaa’i, da Asubah, yana yi musu munanan addu’o’i. (Sahih Al-Bukhaariy: 2814, Sahih Muslim: 677).
Addu’ar da ake yi a cikin irin wannan Al-Qunuut ɗin yana dacewa ne da irin masifar da ta auku. (Subulus Salaam: 1/185).
Amma kuma ba daidai ba ne a riƙa tsawaitawa wurin yin kowane Al-Qunuut fiye da yadda Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi wa Alihi wa Sallam) ya yi. Kamar yadda waɗansu Limamai sukan ɗauki kusan rabin awa, suna yin Qunuut ko na wutri ko na Naazilah! Domin a cikin hakan, akwai takurawa ga jama’ar da suke sallah tare da limamin, baya ga saɓa wa Sunnah.
Mai yin Al-Qunuut da masu amsawa su zama masu ƙanƙan da kai ga Allaah, suna fatar Allaah ya karɓi abin da suke roƙonsa. Don haka, ba daidai ba ne su riƙa rera kalmominsa, kamar yadda mawaƙa suke rera waƙa!
Sannan idan aka samu Allaah Maɗaukaki ya biya buƙatar, watau ya karɓi roƙon, to sai a daina yin addu’o’in.
Shin ko za a riƙa kiran sunayen kafirai ko munafukai ana la’antarsu a cikin Al-Qunuut? Malamai sun ce: Mafi kyawun amsa a nan shi ne: Gara dai a daina yin hakan. Domin shi kansa Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi wa Alaa Alihi wa Sahbihi wa Sallam) da ya yi a farko, ya zo daga baya ya daina, a lokacin da Allaah Ta’aala ya hana shi.
Kuma sai bayan an ɗago daga ruku’u a raka’ar ƙarshe ne ake yin wannan Al-Qunuut ɗin na Naazilah. Haka Ahmad da Abu-Daawud suka riwaito. (Sifatus Salaah: 159).
Kuma a bayyane liman yake yin addu’o’in, ko da kuwa a cikin sallolin da ake yin karatunsu a ɓoye ne, kamar Azahar da La’asar. Su kuma mamu sai su riƙa cewa: Amin! Amin!! Haka ne Al-Bukhaariy da Ahmad suka riwaito. (Sifatus Salaah: 159).
Ana ɗaga hannuwa a lokacin yin addu’o’in, amma bayan an gama sai kawai a sauke su, ba za a shafe fuska da su ba. Domin shafawar ba ta tabbata ba daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi wa Alihi wa Sallam). (Dubi: Silsilah Da’eefah a ƙarƙashin Lamba: 597).
Bayan an ƙare yin addu’o’in sai kawai a yi kabbara a gangara zuwa sujada. Haka Ahmad, da An-Nasaa’iy, da As-Sarraaj, da Abu-Ya’laa suka riwaito da isnadi sahihi. (In ji As-Shaikh Albaaniy, a cikin Sifatus-Salaah: 160).

 *(iii) AL-QUNUUT A SALLAR ASUBAH* 
Abu-Maalik Sa’ad Bn At-Taariq Al-Ashja’iy ya tambayi mahaifinsa ya ce:
‘Baba! Ka yi sallaah a bayan Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi wa Alihi wa Sallam), kuma a bayan Abu-Bakr, da Umar, da Uthmaan, da kuma Aliy a nan Kuufah na kusan shekaru biyar, to ko suna yin Al-Qunuut a Sallar Asubah?’
Sai ya amsa da cewa: ‘Ɗana! Ai wannan ƙirƙirarren abu ne (watau: bidi’a ce)!’Ahmad, da An-Nasaa’iy, da At-Tirmiziy, da Ibn Maajah suka riwaito shi. (As-Shaikh Albaaniy ya inganta shi a cikin Sahih Ibn Maajah:1026, da Irwaa’ul Ghaleel: 435).
Wannan ya nuna yin Al-Qunuut a cikin Sallar Asubah kullum, ba Sunnar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi wa Alihi wa Sallam) ba ce, kuma ba Sunnar Khulafaa’ur Raashiduun (Radiyal Laahu Anhum) ba ce!
Allaah ya kiyaye!
Ga kuma Sa’eed Bn Jubair ya ce: ‘Tabbas! Yin Al-Qunuut a Sallar Asubah bidi’a ce!’ (Dubi tattaunawa a kansa a cikin Irwaa’ul Ghaleel: 436).
Don haka ne malamai irin su Ibn Al-Mubaarak, da Sufyaan At-Thauriy da Is’haaq Bn Raahwiyyah suka ƙyamaci yin Al-Qunuut a cikin Sallar Asubah, in dai ba a lokacin aukuwar wata musiba ba ne!
Wannan shi ne a taƙaice.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Post a Comment (0)