TAMBAYA TA 52

TAMBAYA ======== 👇 asalamu alaikum malam allah yasaka da alheri tambayata itace inada oga kuma shi ogannan nawa kanin babata ne kuma ni yadaura akan harkar center din tamu center scain ce namasu ciki idan bukatar ammafani dakudi ta tashi inayi da aljihuna sannan yakan yi wajen wata biyu bai bani albashiba amma idan yatashi yana biyana harwanda baibaniba sannan duk abin da nakeso yanamin kuma ba acikin kudinaba nikuma wani lokacin musammqn idan yayi tafiya idan inadabukatar abu inadauka acikin kudin amma baya wuce naira dari dari biyu nayi ammfanidashi kuma banafadamai kuma shima ko anyi lissafi bazai tambayan ba ina naira dari biyu koda nadauka dakadan kadanyakai dari biyar sannan munasamu sosai amma tunsanda muka bude wajen haryau baikaramin albashiba duk dacewar samun damuke yi yanzu yqfinadq sosai amma duk bukatuna marasa nauyi idan idan sun taso yakan mun hakan inajin dadi shiiyasa rashin karin albashin baidameniba abindakedamuna shine wannan kudin danakan dauka banafadamai shine hankalina yqkasa kwanciyya inajin karnaje allah yakamani AMSA ===== 👇 Wajibi ne duk dukiyar da aka dora mutum akanta ya biya bukatarsa da kyautatawa, koda kuwa mai wannan dukiyar bai sani ba. Bukatar da ta hada da cin abinci da ruwan sha da hawa mota zuwa inda ake gudanar da wannan sana'ar da Siyan wani abun da bai taka kara ya karya ba. Amma dai wasu sukan iyakance Maka abinda zakake dauka a wannan shagon a kullum, kaga kenan idan ka dauki sama da haka anan Kayi zalunci. Misali, akwai wani da na sani, yake gayamin cewar mai gidansa a kullum ya amince masa ya dauki N200, daga Wannna kuma baya karawa. Sabida wasu idan ka kyale Su sai ranar ya baci, akwai masu neman aure a dukiyar wani. Idan akace neman aure fa, kalma ce mai fadi, ya hada da biyawa budurwarka bukatunta da iyayenta da kawayenta da kannenta da yan uwanta, wani ma har makwabtanta ya dinga musu alheri, kaga nan da nan sai kaga babu shago ba kayan shago. Sabida haka yan Uwa ya kamata muke kula da amanar da aka danka a garemu. Ko idan mutum ya baka kudi a matsayin kuna juyawa, kaima ka samu shima ya samu, sai kaga mutum yana yin sha'anin gabansa, Sabida babu Amana yanzu sai a hankali. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876
Post a Comment (0)