TAMBAYA
========
👇
Assalamu alaikum Barka dawar haka malam ya ayyuka da iyali dafatan komi lahiya.
Malam jiya wata cousin Dina tazo take tambayata wai taji wani wa'azi malamin nabayani akan duba .
Yanacewa inhar mutum zeyi dubane akan sonsanin wani al amari Wanda baidanganci cutarwa ba balefi.
Sannan yakawo misali Wai a zamanin sahabbai ma sunyi duba Dan sugane wani al amari daya kulle Kansu.
Dan Allah malam micece gskyr al amarin
AMSA
======
👇
Tabbas manzon Allah saw ya bayyana mana cewar, daga karshen zamani Allah zai dauka ilimi ta hanyar mutuwar Malamai, daga karshe sai mutane Su riki jahilai suna neman FATAWA a wurinsu, Su kuma suna basu FATAWA ba tare da ilimi ba, Su masu Bada fatawar Sun bata kuma sun batar da wadanda suka nemi FATAWA a wurinsa.
Hakika wannan hadisin ya fara aiki akan wannan malamin. Yanzu abinda muke jira kuma, ki koma wajen wannan malamin ko ki aika masa tambaya ta hanyar radio in a radio kika saurareshi, sai ya sanar damu inda sahabbai sukayi duba, tare da cikakken dalilai.
Allah shine masani.
✍
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876