TAMBAYA TA 55

TAMBAYA ========= 👇 Assalamu Alaikum. malam macece tana zargin mijinta da neman mata sbd wasu lokutan yana shareta inta nemeshi se yace mata yasha shayin buzaye a waje.to se rannan ya aiko da wayanshi mamanshi tanason tayi magana da ita.bayan sun gama waya da ita se text msg ya shigo wayansa ta bude sai taga sakon watace ta turo mishi najin dadin saduwan da sukayi.msg dai gasunan da yawa.wannan sai ya tabbatar mata da zarginta.dan Allah wani mataki ya kamata ta dauka?na gode. AMSA ====== 👇 Subhanallah. Tayi masa wa'azi, ko tayi forwarding din massages din ga duk wanda tasan yana jin maganarsa, Wanda tasan idan yayi masa nasiha zai dena, ba wanda zai tona masa asirinsa ba. Wanda idan ya gani ba wanda zai nunawa, kuma karta nuna masa taga abinda yakeyi. Amma idan hakan shine zaisa ya dena sai ta nuna masa taga duk abinda yake wayarsa. Amma Tabi a hankali, karta daga hankalinta, duk da nasan zataji ciwo. idan kuma bazai dena ba, gaskiya bana goyon bayan taci gaba da zama dashi. Sabida nan gaba ita dashi sai sun zama abin tausayi, maimakon Su zama abin tausayi Su biyu, gwanda shi yaje abin ya kare akansa shi kadai. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876
Post a Comment (0)