TAMBAYA TA 53

TAMBAYA ======== 👇 Assalamu alaikum malam inayi maka fatan alkairi, malam tabayata anan ita ce, za kana ganin hotuna a wayoyi ko a jikin ta karda ance wannan hoton takal min annabi ne ko kuma ace wannan rigar annabi ce s,a,w ko kuma hula ko ra wani ko hoton sawun kafa, to malam wai shin wadanna dagas ke su dinne kuwa, duba da a wancen lkcin babu cemara, shine aduk lkcin da naga irin wannan hotunan a waya sai ina ta wasi wasi, a huta lfy Malam. AMSA ===== 👇 Gaskiya ba Su bane. Kawai mutane ne Sabida sun San hankalinmu akan manzon Allah saw yake, sai suke amfani da wannan damar suke yawo da hankullanmu gabaki daya. Ta yaya a zamanin da babu kyamara wani zaizo Maka da wani hoto yace Maka wai takalmin manzon Allah saw ko rigar manzon Allah ce wannan? Wani ma sai kaga ya dakko hoton wani wani mutum da yayi mummunan hadari jikinsa ya rididdige, sai ya rubuta a kasan wannan hoton ko yayi recording yace wannan mutumin yaci mutuncin manxon Allah s.a.w ne ko ya zagi manzon Allah saw, Allah ya maidashi haka. Kuma babu inda hakan ya faru, domin babu wata jarida da ta buga wannan rehoton, bare kace ga inda abin ya faru. Kuma ma sai Kaji mutum yace idan mutum bai yada Wannan labarin ba Allah zai saukar masa da wani bala'i, kamar wanda akayi masa wahayi akan wannan sakon da yake kokarin yadawa al'umma. Kaga irin wadannan mutanen da suke kirkirar karya suna yadawa, wani Lokacin ma har barazanar suke yiwa mutane with, wai in baka turawa mutum goma ba bala'i zai sameka, Su kuma mutane da yake akwai jahilci da duhun kai a wurinsu da rashin wayewa, sai kaga mutum tana ta yadawa a group da Kuma duk wanda ya sani sai ya tura masa. Wai shi dan ya kubuta daga bala'i da zai sameshi idan bai tura ba. to wallahi wutar irin wadannan mutanen daban take a ranar Alkiyama. Kuma Allah bazai kyale irin wannan iskancin ba. Domin renawa mutane hankali ne. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

1 Comments

  1. Assalamu Alaikum malam ina da tambaya shin koh a gidan tarihi na makka da madina ba asamunsu a can

    ReplyDelete
Post a Comment