TAMBAYA TA 64

*MENENE HUKUNCIN MACEN DATAJE WAJEN MALAMI, HARYA BUQACI WASU SASSA NA JIKINTA?*
:
DAGA ZAUREN
*HISNUL MUSLIM*
:
*TAMBAYA*
Assalamu alaikum mal tambaya ta itace wata matace wani malami yace takawu gashin gabanta dana hammata bayan tabashi sai abin yazo yana damunta abinda yasa tabashi yace zaimata maganin aljanu bayan yakawo abin sai takona sabida taji tsoron abinda tayi to malam yazatayi allah yasaka da alkhairi
:
*AMSA*
wa alaikumussalam
wannan ba malami bane bokane mushriki, akwai hadithin manzan allah (s,a,w)
"Abul Abbas Ibn Taimiyya yace: Al-
arraf suna ne na Boka da mai ilimin
taurari da mai duba (ta hanyar buga
kasa) da makamancinsu, na wadanda
suke magana a kan sanin al’amura ta
wadannan hanyoyi. Kuma Ibn Abbas
yace dangane da mutane masu ilimin
hisabin haruffa kuma suke duba
tafiyar taurari yace bana ganin
wanda ya aikata wannan yana da
wani rabo a gurin Allah.
:
sannan akwai Hadisi ya tabbata acikin Sahihu
muslim.
Manzon Allah yace "Duk wanda ya Je
gurin boka ya tambaye shi wani abu
kuma ya gaskata abin da ya ba shi
labari to ba za a karbi sallarsa ta
kwana arba, in ba " allah ya karemu
:
*ABDUL AZEEZ IBRAHIM*
Abu mujaheed
:
*Masu buqatan shiga Wannan Zaure na hisnul Muslim suyiwa daya daga cikin wadannan number magana ta whatsApp*
*+2348065523065*
*+2349039510396*
Domin Neman Karin bayani akan wata fatawa sai Ku kira wannan numbar↓
*+2347065588557*
(( ﺳُﺒْﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ، ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥْ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ، ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ ((
====================√
Banaka bane kada ka chanja komai, kaji tsoron ALLAH
Kuna iya samun mu ta facebook ta wannan link indanke Qasa
https://mobile.facebook.com/Hisnul-Muslim-667684316700356/?fref=none

Post a Comment (0)