WAYE SHAHRUKH KHAN A BOX OFFICE DA BOLLYWOOD INDUSTRY ?

WAYE SHAHRUKH KHAN A BOX OFFICE DA BOLLYWOOD INDUSTRY
************************************************************************************************


Jarumi SRK ya fara film din sa na farko wato deewana a ranar 25 ga watan June 1992, daga nan yayi Chamatkar da Raju Ban Gaya Gentleman
Wata biyar kacal da shigowa industry ya shiga sahun "A Lister" duk da cewa daga deewana sae Chamatkar ne kadai da shi a kasa

 Da film din deewana, jarumi SRK ya lashe kyautar best male debut
A wannan lokacin ne jaridar Film Trade Magazine a cikin shafin labarin su suka rubuta

""Aamir's appeal has definitely got bruises in the Shahrukh Khan Landslide.""

SRK ya zama mashahurin tauraro, shekara daya a industry wato major Superstar da film din #Baazigar. A lokacin shine biggest star na biyu bayan sunny deol. Kamar yadda wani abokin chunky pandey yake cewa

"some stage at baazigar and darr time you knew he was there at the top."

A darr, SRK ya tafi da dukkan yabo daga yan kallo da crtics sanadiyyar cinye sunny deol da ya yi, duk da cewa Sunny Deol ne lead actor, number one box office star, ga kuma SRK a negative role, role din da kusan kowane jarumi a lokacin ke tsoron karÉ“a saboda gudun samun matsala da fanbase da suka fara ginawa 

A tsakanin August 1993 zuwa August 1996, Sunny deol yana da films guda tara. A cikin su, guda biyar flop suka yi, biyu sukai disaster, darr ne kawai yayi nasara and the credit went to SRK. Kamar yadda box office India suka taba cewa

"public was with Shahrukh Khan's character in these films & sympathy went to him which made him a major star"

Bayan baazigar da darr, SRK ya hada fanbase/fan following masu yawan gaske. Hakan ya zama karo na farko a shekaru sha biyar da Amitabh Bachchan ya samu close marking a bangaren fan following.

SRK ya lashe kyautar filmfare award for best actor da baazigar. Role na Anti hero baya nasara a baya. Hatta Amitabh Bachchan da Dilip kumar sun gwada basu dace ba. SRK ne ya karya wannan kwarin. Ya zamto sa'a ga Yash Raj Films da yash Chopra. Kamar yadda yash Chopra a wani interview aka taba tambayar sa

" I remember after release of Dilwale dulhaniya le jayenge you told me that you had never seen so much money in your life"

Yash Chopra ya amsa da cewa

" its true... DDLJ has done many things for me. It has helped us realized so many of our dreams. When I came to realise that distributors aren't quite upfront in their dealings, I decided to become my own distributor. For the first time we saw big money, I asked my son what he wanted, he said he wanted that we should have our own studio. Today we are ready to open our own state-of-the-art studio.... thanks to DDLJ"

Kabhi Haan Kabhi Naa ya zama ready tun a may 1992, shi ya kamata ya zama Debut na SRK, amma saboda rashin masu saye dole aka ajiye shi. A February 1994 bayan SRK ya zama box office star, film ya fita da sunan SRK, ya saida kansa, aka samu nasara
 Kabhi Haan Kabhi Naa ya zama semi hit a box office. Anjaam ya zama average success amma bai samu zama babban Hit ba. Anjaam ya hada footfalls fiye da wasu Multistarrer hits a 94 irin su Yeh dillagi. An saida shi da tsada ne saboda big starcast da aka hada a film din (SRK and madhuri)
 A lokacin wasu jarumai mata suka magana a kan sa. Mamta take cewa

"Shahrukh has a tremendous fan following

Meenakshi tace

" His magnetism is what makes him special"

Sonali bendre ma tace

"He is a very good human being and a good actor

Wata babbar jarida tayi rubutu a kan sa inda tace

HOTTEST MALE STAR
Invincible Khan

From Fauji boy to an obsessed killer, Shahrukh khan has achieved many success than even he could imagined for himself." 

A December 1994 kuma gidan television na star TV a wani show nasu na karan Arjun suke cewa

" For the first time #Unsalable Salman dares destiny by being cast opposite #Sellout Shahrukh,"

A 1995 karamin film da karamin budget ram Jaane ya yi clashing da babban budget na Aamir khan wato Akele hum Akele tum, kuma ya cinye clash din, kamar yadda a lokacin Box office India suka rawaito cewa 

"Akele hum Akele tum was expected to do better before release due to the combination of Aamir khan and mansoor khan, the combo delivered a huge hit with Qayamat Se Qayamat tak and fair runner jo jhita wohi sikandar, the music had scored and the film had been well promoted by venus but the action masala ram Jaane with Shahrukh Khan easily outshoned Akele hum Akele tum..... Ram Jaane was ahead from day one and remained ahead to the end. Ram Jaane also managed to fare better in overseas despite Akele hum Akele tum having more overseas friendly genre. Akele did better in Us/Canada but was dull in United Kingdom where Ram Jaane was much better "

Films din SRK guda biyu karan Arjun da Trimurti suka balla opening records gaba daya tun daga opening day zuwa opening weekend. Duk a shekara guda. Trimurti shine ya fara kawo 1 crore opening day a tarihin box office.Tun daga 1976 zuwa 2018 tsawon shekaru Arba'in da biyu kenan (42 years) SRK shi yake da record na jarumin da yafi kowanne jarumi saida tickets a shekara guda. Ya saida average ticket da ta haura 10 Crore, wato 10 Crore Footfalls. A Nett Adjust da inflation na yau zai bada 1100Cr+ In a single calendar year. 
A tsawon shekara Arba'in da biyu dinnan Bayan SRK din babu wanda ya kara hada 10 Crore Footfalls a shekara guda,

Mu hadu a cigaban labarin, wannan wasa farin girki ne......

AKK
Post a Comment (0)