HUKUNCIN ADDU'A TSAKANIN HUDUBAR JUMA'A TA FARKO DA TA BIYU

*_HUKUNCIN ADDU'A TSAKANIN HUDUBAR JUMA'A TA FARKO DA TA BIYU !!_*


                               *Tambaya:*
Assalamu alaikum malam ya gida ya kuma dawainiya dafatan kowa lfy Allah yasa haka ameen, mal ina da tambaya ne akan halaccin addu'a da akeyi tsakanin huduban farko da na karshe, Allah yasaka alkhairi.


                                   *Amsa*
Wa'alaikum assalam To dan'uwa Annabi ﷺ yana cewa: "A ranar juma'a akwai wani lokaci wanda babu wanda zai dace da shi, ya roki Allah a lokacin, face sai ya amsa masa" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 893.

Malamai sun yi sabani game da wannan lokacin zuwa wajan zantututuka arba'in, kamar yadda Ibnu Hajar ya hakaito a Fathul-bary, 2\419, daga cikin wadannan maganganun akwai cewa: tsakanin hudubobin juma'a guda biyu lokacin yake fadowa.

Don haka wasu malaman suke ganin mustahabbancin yin addu'a tsakanin hudubobi biyu, saboda musulmi zai iya dacewa da wancan lokacin mai falala.

Allah ne mafi sani.

2\3\2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

 ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07
036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)