HANYOYIN SHIGA ALJANNA 1


HANYOYIN SHIGA ALJANNA NA 1

Anas ɗan Malik Allah ya ƙara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce:" Duk wanda ya roƙi Allah Aljanna sau uku, Aljanna za ta ce: Ya Allah ka shigar da shi Aljanna, kuma wanda ya nemi tsari daga shiga wuta sau uku, wuta za ta ce: Ya Allah ka tseratar da shi daga wuta" Hadisi ne ingantaccce; Tirmizi da Ibnu Maja ne suka ruwaito.

Fa'ida: wannan hadisin shi ne na kusa da na ƙarahe a cikin sunanu Ibnu Maja.

Jama'a mu yawaita roƙon Allah Aljanna, da neman tsari daga wuta.

ABU RAZINA PAKI
Post a Comment (0)