ALLAH BAI KAYYADE LOKACIN RAMA AZUMI BA !!!

ALLAH BAI KAYYADE LOKACIN RAMA AZUMI BA !!!


*Tambaya*

Assalamu alaikum, Dr. Mace ce ta sha Azumin shekara uku ajere saboda ciwon ulcer, kuma abin da zasu kai baki gagaransu yake ballatana ta ciyar. Menene mafita? 

*Amsa*

Wa alaikum assalam Ta jira har Allah ya bata lafiya sai ta rama. 
Allah madaukakin sarki a cikin Suratul Bakara aya ta: (185) ya sanya ramuwar azumi ga mara lafiya a wasu kwanaki na daban don ya nuna abin a bude yake, zuwa lokacin da aka samu dama, ba tare da yin sakaci ba. 

Allah ne mafi sani

*Amsawa*

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
03/03/2018

Domin samun fatawoyin Malam Kai tsaye sai a kasance damu a 

FACEBOOK⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

TELEGRAM⇨
https://t.me/Miftahulilm2

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)