KA'IDOJIN HADDACE ALQUR'ANI

KA’IDOJIN HADDACE AL-QUR’ANI

Tambaya :

Assalamu alaikum, malam don Allah ni karamin dalibi ne, ban dade da fara hadda ba, shi ne nake so a taimaka min da hanyar da zata kai ni zuwa haddace Alqur'ani.

Amsa :

Wa alaikum assalam To dan'uwa, ina fatan Allah ya datar da kai zuwa alkairi, ga wasu daga cikin hanyoyin da za su taimaka maka, wajan hadda, mutukar ka kiyaye su, to za ka samu hadda mai kwari :

*1. Ya wajaba ka rinka yin hadda a wajan malami saboda ya dinga gyara maka. 

*2. Idan za ka fara hadda ka fara daga suratu Annas saboda ta fi sauki. 
    
*3. Ka da ka dinga haddace abu mai yawa, musamman farkon fara haddarka, saboda wannan  zai jawo ka yi hadda mara karfi, ya kamata ka dinga yi daidai yadda zaka iya yin muraja’a  , don ka inganta haddarka.

*4. Ka rinka yin hadda da al-qur’ani iri daya, saboda hakan zai taimaka ka dinga tuna gurin da kowacce aya take, da kuma tuna inda kowanne shafi ya ke karewa.

*5. Duk lokacin da ka haddace izu daya, to kar ka wuce shi, har sai ka maimaita shi a kalla sau ashirin, kafin ka dora  na gaba.

*6. Idan haddarka ta yi zurfi, to ka samu wanda za ku dinga yin muraja'a da shi, domin wannan yana taimakawa wajan karfin hadda yadda ya kamata.

Don neman Karin bayani, duba :  khuduwatun ilassa’adah  200-201
Allah ne ma fi sani

Amsawa✍🏻

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
5/1/2015

Daga ZAUREN FIQHUS SUNNAH

Post a Comment (0)