WANDA BA A RUFE SHI DA WURI BA, YAUSHE ZA A YI MASA TAMBAYAR KABARI ?

WANDA BA A RUFE SHI DA WURI BA, YAUSHE ZA A YI MASA TAMBAYAR KABARI ?


Tambaya:
السلام عليكم ورحمة الله
 ÙˆØ¨Ø±ÙƒØ§ØªÙ‡ 
Malam barka da rana, 
Yara suka yi min tambaya sun ga ana ta yawo da gawar sarauniyar Ingila, shi ne su ka ce ya tambayar da akeyi a kabari ga shi ba a binne ta ba, Kuma irin mutuwar ba a ga gawar su ba balle a binne, ya ta su tambayar za ta kasance?

Amsa
Wa alaikum assalam
A zahirin nassoshin Sharia, sai an binne mutum ake yi masa tambayar kabari.ko kwana nawa aka yi ba a binne gawa ba, sai an binne ta za a yi mata tambayoyin Munkar da Nakiru.

Wanda Zaki ko kura ta cinye, kabarinsa shi ne cikin dabbar, Allah Mai Iko ne ya tattara shi ayi masa tambayoyin KABARI kamar yadda malamai su ka Yi bayani.
Allah Ne Mafi sani

Dr Jamilu Yusuf Zarewa
14-9-2022

Miftahul ilmi 

Facebook ⇨https://www.facebook.com/Miftahulilmi.ml

TELEGRAM ⇨https://t.me/miftahulilmii

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)