NA TSINCI ZOBEN ZINARI AMMA NA SIYAR DA SHI

*_NA TSINCI ZOBEN ZINARE, AMMA NA SIYAR DA SHI?_*


                               *Tambaya*
Assalamu alaikum. Allah kara ma malam lfy,tambayata itace shekara 3 da tsintan zoban zinare har yau ba,asami me zoban ba sai akakai kasuwa aka saida.to wannan kudin ya za,ayi dashi.

                                     *Amsa*
Wa'alaikum assalam, Idan aka yi tsintuwar da ta Kai cigiya, ya wajaba a sanar da sifofinta tsawon shekara guda, daga nan sai ayi amfani da ita in ba'a samu mai ita ba, kamar yadda ya tabbata a hadisi.

A bisa hadisin da ya gabata za ki iya amfani da kudin da kika siyar, saidai idan mai ita ta zo daga baya za kı biya ta, in kuma ba ta zo ba, to arziki ne, Allah ya koro miki daga falalarsa.

Allah ne mafi sani.

6/04/2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)