*_MACE ZATA IYA DAGA MURYARTA DA KARATUN SALLAH?_*
*Tambaya:*
Assalamu alaikum Malam barka da yau, tambaya zan yi malam. Shin ya halatta mace ta daga murya a cikin karatun sallah kuwa???
*Amsa*
Wa'alaikum assalam, To dan'uwa ya halatta a gare ta ta daga muryarta yayin karatun alqur'ani a sallah, sai in akwai wanda ba muharrami ba a kusa, to sai ta yi kasa da muryarta, don kar ya fitinu.
Wasu malaman sun haramta mata bayyana karatu, in ta ji tsoran fitina, saboda Annabi ﷺ ya umarci mata da yin tafi a sallah, lokacin da liman ya yi rafkannuwa, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1145, sai suka fahimci cewa: Annabi ya umarce su, su yi tafi ne, don kar wadanda ba muharramai ba, su ji sautinta.
Mace tana daukar hukuncin namiji a cikin dukkan hukunce-hukuncen shari'a, in har ba'a samu nassin da ya kebance ta ba, wannan ya sa za ta bayyana karatu a wuraren da yake bayyanawa, in ba'a ji tsoron fitina ba.
Allah ne mafi sani.
13\5\2015
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.