YA AURE TA TANA DA CIKIN IDDA MIJIN BAI SANI BA

*_YA AURETA TANA CIKIN IDDA, MIJIN BAI SANI BA_*

                                *Tambaya*
Wani Mutun ne yayi aure bayan sun dau wasu kwanaki da Matar kuma sun samu alaqa ta aure sai kawai take cewa mijin nifa har yanzu bangama Idda ba.

                                 *To shin:-*
1= Menene Matsayin haduwar dasu kai?
2= Menene Matsayin Aurensu ayanzu?
3= Menene Hukuncin Mijin?
4= Menene Hukuncin Matar?
5= Idan Allah yaqaddara da samun Ɗa a tsakaninsu memene matsayin dan?
Allah yataimaka.

                                      *Amsa*
Babu shakka da akwai sakaci na iyayen matar, kuma matar tayi babban laifi ta saba ka'idar da Allah SWA ya saka ga mai Iddah, kuma taci amanar mijin da ya sake ta bata gama idda ba ta auri wani.

                                   *Hukunci*
1- Haduwar da sukayi ta Aure ita matar ga sabawa Allah SWA shi kuma mijin bashi da laifi idan har bai saniba.

2- Auren da sukayi Aurene kan aure mijin ta na da ya na da damar dawo da matarsa matukar bata fita daga idda ba tana nan a matsayin matarsa.

3- Shi kuma mijin bashi da laifi matukar bai saniba. 

4- Ita kuma matar ta tafka kuskure mai girma dan haka sai ta tuba tayi nadama tsakaninta da mahaliccinta sabo da ta karya dokar da ya shinfidawa bayinsa.

5- Dan da suka haifa dansu ne kuma yana da gadon kowa daga cikinsu matukar shi uban ya amince dan sane.

*ALLAH YA SAWAKE YA KUMA SHIRYAR DAMU.*

Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)