ZAN IYA JINKIRTA SALLOLI HAR ZUWA LOKACIN BACCI?

*_ZAN IYA JINKIRTA SALLOLI HAR ZUWA LOKACIN BACCI?_* *Tambaya* Assalamu alaikum, Malam Ina jinkirta sallah ISHSHA Sai nazo bacci, shin hakan ya dace? *Amsa* Wa'alaikum assalam, bai halatta ga musulmi ba ya ji kıran sallah, ya ki tashi ya tafi masallaci, in ba da wani uzuri ba, Allah yana cewa a cikin suratun Nisa'i aya ta:103 "Tabbas sallah wajibi ce akan muminai a çıkın lokuta kayyadaddu". Jinkirta sallah daÄŸa lokacinta yana çıkın tozartata, Allah ya yi alkawarin saka wadanda suke tozarta sallah a wani kwari a cikin wuta, kamar yadda aya ta: 169 a suratul A'araf ta tabbatar da hakan. Tozarta sallah alama ce ta tozarta ragowar aiyukan alkairi, saboda ita ce ginshikin addini, duk Wanda ya kiyaye Allah zai kiyaye shi, wanda ya kiyaye Allah zai same shi a gabansa. Allah ne mafi Sani. 2/5/2016 Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa. Gabatarwa:- ÃbûbäkÃ¥r Êkâ. Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. ______________________________________ » Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp). ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)