HUKUNCIN BIRTHDAY A MUSULUNCI

*_HUKUNCIN HAPPY BIRTHDAY !!_* *Tambaya* Assalamu Alaikum. Dr ina yimaka fatan alkhairi Gameda hukuncin murnar zagayowar ranar haihuwa [Birthday]. Wasu na ganin bidi'a ne, wasu kuma na ganin ba bidi'a bane tunda ba addini bane kuma wanda yayi baya tsammanin samun lada daga ubangiji To malam yaya Al'amarin yake? Kahuta lafiya *Amsa* Wa'alaikum assalam, a zahirin gaskiya happy birthday ya fi kama da al'ada, saboda ba wanda yake yinsa da nufin ibada ko neman lada da kusanci da Allah, ita kuma bidi'a tana shiga addini ne kawai. Ya halatta a farar da abin da babu shi a zamanin manzon Allah, mutukar ba'a ibada ba ne ba'a kuma nufaci lada da shi ba, wannan yasa amfani da Radio da Makirfon da jirgi da carbi ya halatta duk da cewa babu su a zamanin mazon Allah (SAW) Saidai duk da haka barin HAPPY BIRTHDAY shi ne ya fi zama daidai saboda duk lokacin da ranar haihuwar mutum ta zagayo yana kara kusantar kabari ne rayuwarsa kuma ta ragu, don haka yin bakin ciki a irin wannan yanayin shi ne ya fi fiye da nuna farin ciki. Magabata nagari sun kasance suna bakin ciki duk lokacin da suka tina wani bangare na rayuwarsu ya shude, Hasanul-basry yana cewa: (Ya kai dan'adam ba wani abu ba ne kai sai yininnika, duk lokacin da wani yini ya wuce wani bangarenka ya tafi. Haramta Birthday da bidi'antar da masu aikatata yana bukatar dalilin sharia, saboda babin al'adu a bude yake har sai an samu dalilin haramci, don haka ya halatta, tare da cewa nuna bakin ciki idan ranar haihuwar ta zagayo shi ya fi fiye da nuna farin ciki saboda abin da ya gabata na aikin magabata na kwarai. Allah ne mafi sani. 13/3/2018 Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa. Gabatarwa:- ÃbûbäkÃ¥r Êkâ. Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. ______________________________________ » Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp). ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)