YA SAKE MU SAKI DAYA SAI YA MUTU KAFIN MU GAMA IDDA, KO MUNA DA GADON SA?

*_YA SAKE MU SAKI DAYA, SAI YA MUTU KAFIN MU GAMA IDDA, KO MUNA DA GADONSA?_*

                                 *Tambaya*
Malam mutum ne yana cikin halin rashin lafiya, ya saki matansa har guda biyu saki daya, kuma bai dawo da su  ba har ya mutu, kuma ba su gama iddah ba, yaya za'a yi ? za su yi masa takaba, kuma suna da gadonsa, ko ko a'a ?

                                    *Amsa*
To dan'uwa mutukar yadda ka sifanta, haka abin yake, to za su bar iddar saki, su koma iddar mutuwa, kuma za su ci gadonsa, saboda suna nan a matansa, tun da saki daya ne, Ibnu-khudamah ya hakaito ijma'in malamai akan haka.

Don neman Karin bayani duba: Al-mugni 8\94.

Allah ne mafi sani.

9\5\2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)