BA'A IDDAR SAKI DA WATA UKU

*_BA'A IDDAR SAKI DA WATA UKU!!!_*

                                 *Tambaya:*
Assalamu Alaikum Malam ina da tambaya don Allah mace ce tana shayarwa amma bata jini, sai mijinta ya sake ta, to wai za ta kirga watannin ne na iddanta ko ya zata yi?.

                                     *Amsa:*
Wa'alaikum assalam, Idan aka saki mace tana shayarwa, ya wajaba ta jira tsarki uku, ko da kuwa za ta yi shekara uku kafin ta gama, Ba'a idda da watanni uku sai ga wacce ba ta fara haila ba, ko kuma wacce ta yanke kauna daga haila saboda tsufa, kamar yadda aya ta: 4 a suratu Addalak ta tabbatar da hakan.

Allah ne mafi Sani.

22/04/2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)