WANDA YA MUTU YANA SHAN TABA BAI TUBA BA

*_WANDA YA MUTU YANA SHAN TABA SIGARI, BAI TUBA BA?_*

                               *Tambaya*
Assalamu Alaykum, Ina fatan Dr yana Lafiya. Dan Allah mene ne Hukuncin Mai shan taba (sigari), har ya mutu bai tuba ba?. Na gode.

                                   *Amsa:*
Wa'alaikumus salaam wa rahmatullahi wa barakaatuhu, Dukkan wanda ya mutu yana shan taba (sigari) bai tuba ba, yana karkashin ikon Allah, in ya so ya gafarta masa, in ya so ya kama shi da zunubin shan tabar da ya yi, saboda shan taba haramun ne, saboda ta kunshi cuta, kuma duk abin da yake cuta ne tsantsa haramun ne, kamar yadda ayoyin Alqur'ani da hadisan manzon Allah suka tabbatar.

Allah ne mafi sani.

11/05/2016
03/08/1437

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)